Dollar

40,5651

0.02 %

Euro

47,1471

-1.18 %

Gram Gold

4.324,0300

-0.65 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Rundunar sojin Sudan da ke samun goyon bayan gwamnatin ƙasar ta yi Allah wadai da kafa gwamnatin adawa ta RSF, inda ta bayyana ta a matsayin "gwamnatin fatalwa"

Sudan ta yi Allah wadai da kafa gwamnatin adawa ta RSF

Sudan ta yi Allah wadai da sanarwar da rundunar dakarun sa kai ta Rapid Support Forces (RSF) ta fitar ta kafa gwamnatin adawa.

A wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, ma’aikatar harkokin wajen Sudan ta bayyana matakin na RSF a matsayin ‘‘babban raini da nuna halin ko-in-kula ga wahalhalun al’ummar Sudan, waɗanda suka jure duk wani nau'i na tashin hankali, zalunci da azabtarwa a hannun waɗannan 'yan ta'adda".

Yayin da ta kwatanta gwamnatin da RSF ke jagoranta da “gwamnatin fatalwa” ma’aikatar ta ce matakin “alamu ne karara na shan kaye da kuma fatattakar ‘yan tawayen a hannun manyan sojojinmu”.

Kazalika ma’aikatar ta bayyana gwamnatin RSF a matsayin "gwamnati marar doka".

A watan Fabrairu ne dai dakarun RSF da wasu shugabannin ƙungiyoyin 'yan tawayen da ke ƙawance da su, suka amince da kafa gwamnati don kafa sabuwar Sudan, da nufin ƙalubalantar halaccin gwamnatin da sojoji ke jagoranta.

Ta yaya aka kawo wannan gaɓa?

A ranar Asabar ne, gamayyar dakarun ƙungiyoyin kafa ƙasar Sudan waɗanda RSF ke jagoranta, suka sanar da kafa gwamnatin adawa ƙarƙashin kwamandan RSF Mohamed Hamdan Dagalo.

Gamayyar ta kuma nada Mohamed Hassan al-Ta'ayshi - tsohon mamba a majalisar riƙon ƙwarya ta Sudan daga shekarar 2019 har zuwa juyin mulkin soji na 2021 - a matsayin firaminista a wani mataki da ta kira da "gwamnatin zaman lafiya da haɗin kai".

Wani mamba na RSF ya shaida wa AFP bisa sharaɗin sakaya sunansa cewa yanzu al-Ta'ayshi zai fara kafa majalisar ministoci.

Rundunar sojin Sudan ƙarƙashin jagorancin babban hafsan sojan kasar Janar Abdel Fattah al Burhan, ta yi Allah wadai da matakin RSF na kafa gwamnatin adawa, tare da yin alƙawarin ci gaba da yaƙi har sai ta karɓi ikon dukkan sauran yankunan Sudan da ke fama da tashe-tashen hankula da yunwa.

Wa ke iko a Sudan?

A halin da ake ciki a yanzu, Sudan ta rabu, inda sojoji ke iko da yankin arewa, gabashi da kuma tsakiya - bayan da suka sake ƙwace babban birnin ƙasar, Khartoum.

Yayin da ɓangare guda, rundunar RSF ke riƙe da ikon yawancin yankunan yammacin ƙasar kamar yankin Darfur mai faɗi da wasu yankuna amma sojojin ƙasar na ci gaba da fatattakar su daga tsakiyar Sudan.

Gwamnatin da ƙasashen duniya suka amince da ita na soja da aka kafa a watan Mayu kuma ƙarƙashin jagorancin tsohon jami'in Majalisar Ɗinkin Duniya Kamil Idris, inda har yanzu ba a cika muƙaman majalisar ministoci uku ba.

Me hakan zai iya haifarwa?

Jami'an Majalisar Ɗinkin Duniya sun yi gargaɗin cewa kafa gwamnatin adawa ta RSF a yanzu tare da firaminista da majalisar shugaban ƙasa - na iya zurfafa rarrabuwar kawuna a Sudan tare da dagula ƙoƙarin diflomasiyya na kawo ƙarshen rikicin ƙasar, wanda ya fara a watan Afrilun 2023.

Tun dai daga watan Afrilun 2023 ne yaki ya ɓarke tsakanin dakarun sojoji Sudan da RSF, lamarin da ya laƙume rayukan sama da mutum 20,000 tare da raba mutane miliyan 14 da muhallansu, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya da hukumomin yankin.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#