Dollar

40,5954

0.02 %

Euro

46,5782

0.52 %

Gram Gold

4.313,6500

0.93 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Baya ga bama-baman da aka ƙwato, sojojin sun kuma ƙwace bindigogin AK-47 da bindigogin PKT daga hannun 'yan ta'addar.

Sojoji sun kama ‘yan Boko Haram da suka yi yunƙurin ɗana bama-bamai a wata gada a Borno

Dakarun sojojin Nijeriya sun samu nasarar cafke 'yan ta'addar Boko Haram a yayin da suke yunƙurin tayar da bama-bamai a wata gada da ke kan hanyar Dikwa zuwa Marte a jihar Borno.

Samamen ya kai ga ƙwato manyan bama-bamai guda biyu bayan an ɗauki tsawon lokaci ana gwabza faɗan.

Wannan ci gaban dai na daga cikin hare-haren da dakarun rundunar haɗin gwiwa ta shiyyar Arewa maso Gabas, na Operation Hadin Kai ke ci gaba da kaiwa, da nufin kawar da ‘yan ta’adda daga yankin.

Da yake magana da gidan talabijin na Channels, Kwamandan rundunar Operation Hadin Kai, Manjo Janar Abdulsalam Abubakar ya bayyana cewa a cikin makon da ya gabata, sojoji sun gudanar da gagarumin samame na kakkaɓe miyagu daga yankin Tafkin Chadi da Dajin Sambisa da Tsaunukan Mandara.

“Lokacin da sojojinmu ke kan hanyar Dikwa-Marte sun yi arangama da ‘yan Boko Haram da ke kokarin sanya bama-bamai a kan wata gada, nan take sojojin suka yi musu luguden wuta wanda ya tilasta musu barin bama-baman suka gudu.

“An samu kwanciyar hankali a yankin Tafkin Chadi, saboda ‘yan ta’addan sun yi ta tserewa mu kuma muna fafararsu.

“Ba za mu bari su sake kai wa sojojinmu hari ba, duk al'ummomin da aka ƙwato ba za su sake faɗawa hannun 'yan ta'adda ba, sojojinmu na da kwarin gwiwa kuma a zaƙe suke," in ji Manjo Janar Abubakar.

Wadannan hare-hare sun yi sanadin kashe ‘yan ta’adda tara a kananan hukumomin Bama, Gwoza, da Konduga a jihar Borno.

A cewar Manjo Janar Abubakar, sojojin ruwa da ke gaɓar Tafkin Chadi, da sojojin ƙasa, da kuma sojojin saman Nijeriya da ke bayar da sahihin tallafi ne suke gudanar da ayyukan hadin gwiwa a lokaci guda.

Baya ga bama-baman da aka ƙwato, sojojin sun kuma ƙwace bindigogin AK-47 da bindigogin PKT daga hannun 'yan ta'addar.

Kwamandan rundunar ya lura cewa hare-haren da aka ci gaba da kaiwa sun inganta sosai da kwanciyar hankali da tsaro a yankunan kan iyaka da ke kusa da iyakar Tafkin Chadi.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#