Dollar

40,6696

0.08 %

Euro

46,4490

-0.14 %

Gram Gold

4.308,5800

0.21 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Shirin Samar da Abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce daga yau Alhamis zai daina raba tallafin abinci a arewa maso gabashin Nijeriya sakamakon ƙarancin kuɗaɗen tallafi da shirin ke fuskanta

MDD ta daina rabon tallafin abinci na shirn WFP a arewa maso gabashin Nijeriya

Shirin Samar da Abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya (WFP) ya bayyana cewa daga yau Alhamis zai dakatar da dukkan agajin gaggawa na bayar abinci da kayayyakin gina jiki ga mutum miliyan 1.3 a arewa maso gabashin Nijeriya.

Wannan matakin ya biyo bayan ƙarancin kuɗaɗen tallafi da shirin ke fuskanta, a daidai lokacin da tashe-tashen hankula ke ƙaruwa.

A cewar wata sanarwa daga shirin na WFP, kayan abinci da magunguna na shirin sun ƙare gaba ɗaya.

WFP ɗin ya ce abinci na ƙarshe da suke da shi ya bar ɗakin ajiyarsu a farkon watan Yuli, haka kuma za su daina aikin ceto baki ɗaya idan aka kammala rabon abincin da ya rage.

Ba tare da tallafin gaggawa ba, mutane masu rauni da dama za su fuskanci rashin mafita da faɗawa cikin yunwa mai tsanani da yin hijira, ko kuma faɗawa hannun ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi.

Shirin na MDD ya ce idan ba a samu kuɗi nan take an ci gaba da wannan aikin ba, mutane za su shiga cikin wani hali mai tsanani, inda za su fuskanci yunwa, wasu su yi hijira da kuma yiwuwar ƙungiyoyin ta’ddanci su yi amfani da wannan dama.

Yara ƙanana ne za su fi shan wahala idan aka dakatar da wannan tallafi mai muhimmanci.

Fiye da asibiti 150 da WFP ke tallafa wa a jihohin Borno da Yobe za su rufe, wanda hakan zai katse magungunan ceton rai ga yara fiye da 300,000 da shekarunsu bai kai biyu ba, kuma hakan zai ƙara saka su cikin haɗarin mutuwa.

A yankunan da rikici ya shafa, ƙaruwar tashin hankali daga ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi na haifar da yawaitar ƙaura.

Mutane kusan miliyan 2.3 a yankin Tafkin Chadi sun tsere daga gidajensu, wanda hakan ke ƙara matsin lamba kan taƙaitattun albarkatun ƙasar da ake da su.

 

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#