Sport
Dollar
40,6711
0.08 %Euro
46,4203
-0.18 %Gram Gold
4.308,5800
0.21 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Yankin Kolmani, wanda ke kan iyakar jihohin Bauchi da Gombe, nan ne muhimmin wurin da aka fara samun mai a arewacin Nijeriya.
Kamfanin man Nijeriya NNPCL ya ce ya tona rijiyoyin mai huɗu a Kolmani da ke kan iyakar jihohin Bauchi da Gombe a wani mataki na ƙara faɗaɗa neman mai da iskar gas a arewacin Nijeriya.
Yusuf Usman, wani darakta a kamfanin NNPC, ne ya bayyana wannan a wani taro na tattaunawa tsakanin gwamnati da ‘yan ƙasa da gidauniyar tunawa da Ahmadu Bello ta shirya a Kaduna ranar Laraba.
Usman ya ce a halin yanzu kamfanin yana duba irin fasahar da ta fi dacewa domin amfani da ita a mataki na gaba na tono a filin haƙar mai na Kolmani.
Ya kuma jaddada jajircewar NNPC wajen haɓaka harkar mai da iskar gas a faɗin arewacin ƙasar.
“Kawo yanzu, kamfanin NNPC ya tona rijiyoyin mai huɗu a Kolmani da ke jihar Bauchi kuma yana nazari kan fasahar da ta fi dacewa ya ƙaddamar a mataki na gaba na ayyukan tono,” in ji Usman.
A wani ɓangare na aikinsa wajen tallafa wa dabarun gwamnatin tarayya na bambanta hanyoyin samun makamashi, ya ƙara da cewa NNPC na gina tashoshin iskar gas na CNG da LNG a jihar Kogi.
Ana sa ran ayyukan su inganta samun makamashi a arewacin ƙasar da kuma tallafa wa shirin gwamnatin Tinubu na mayar da ƙasar mai amfani da makamashi da suka fi tsafta.
Filin Kolmani, wanda ke kan iyakar jihohin Bauchi da Gombe, nan ne muhimmin wurin da aka fara samun mai a arewacin Nijeriya.
A watan Mayun shekarar 2025, NNPC ya yi shelar shirye-shiryen fara ayyukan tono a filin.
Comments
No comments Yet
Comment