Sport
Dollar
40,6701
0.08 %Euro
46,4215
-0.18 %Gram Gold
4.308,4000
0.2 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Wasu bidiyoyi da ke yawo a shafukan sada zumunta sun nuna ‘yan Ghana suna zanga-zangar neman hukumomi su kori ‘yan Nijeriya daga ƙasarsu kan zargin da suka yi cewa halayen ‘yan Nijeriyar ba su dace da al’adun ƙasar Ghana ba.
Hukumar da ke kula da ‘yan Nijeriya a ƙetare (NiDCOM) ta yi kira da a kwantar da hankali game da zanga-zangar ‘yan Ghana da ke zargin cewa ‘yan Nijeriya ne ke aikata laifuka a ƙasar.
Wata sanarwa da mai magana da yawun NiDCOM ya fitar ranar Talata ta ambato shugabar hukumar, Abike Dabiri-Erewa, tana sukar abin ta bayyana a matsayin “yin kuɗin-goro” ga ‘yan Nijeriya a matsayin masu aikata laifuka a Ghana.
“’Yan Nijeriya ba masu aikata laifuka ba ne. Jakadu na gari ne a duk inda suke yayin da ya kamata a zaƙulo ɓata-gari domin su fuskanci hukunin da ya dace,” kamar yadda sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Abdur-Rahman Balogun, ya fitar ta ce.
“’Yan Ghana da ‘yan Nijeriya tamkar tagwaye ne. ‘Yan’uwa ne a tafiyar ECOWAS kuma ya kamata a ci gaba da harkar haɗin kan yanki domin a zauna lafiya kamar ‘yan’uwa.”
Wasu bidiyoyi da ake yaɗawa a shafukan intanet sun nuna wasu ‘yan Ghana suna zanga-zanga inda suka yi kira ga hukumominsu da kori ‘yan Nijeriya daga ƙasar kan zargin yin ɗabi’un da ba su dace da al’adun Ghana ba.
Sai dai kuma, Dabiri-Erewa ta yi kira ga ‘yan Nijeriya mazauna Ghana cewa ka da su bari wannan matakin zanga-zangar ya fusata su ko kuma su shiga tashin hankali. Ta tabbatar musu da cewa hukumomin ƙasar suna aikin shawo kan matsalar.
Yayin da take ba da shawara cewa ya kamata ɓangarorin biyu su kauce wa amfani da kalamai masu tunzura mutane, shugabar hukumar ta ce irin waɗannan kalaman ka iya sa lamarin ya ta’azzara.
Ta nemi ‘yan Nijeriya su yi watsi da bidiyoyin da ke yawo da ke nuna cewa ana lalata shaguna da gidajen ‘yan Nijeriya.
“Babu hujjar da ta tabbatar da haka, kuma dole mu yi ƙoƙarin hana ramuwar gayya ta ko wace hanya,” in ji shugabar ta NiDCOM.
Comments
No comments Yet
Comment