Hukumomi sun ce an shawo kan matsalar a birnin Rumbek, kuma an kama fararen hula huɗu ɗauke da bindigogi sakamakon mummunar arangamar a safiyar Juma'a.
Gwamnatin Sudan ta Kudu ta ce sojoji suna cikin mutane 71 da aka kashe a wani mummunan rikici da ya faru a ranar Juma'a a tsakiyar garin Rumbek.
Shaidu sun bayyana wa AFP cewa wasu matasa daga wajen Rumbek sun yi yunƙurin ƙwace garin har ma sun yi nasara ta ɗan lokaci.
Bayan da 'yansanda da sojoji suka isa, maharan sun janye, kuma shaidu biyu sun ce faɗan ya koma wajen iyakokin birnin.
"Fararen hula ɗauke da makamai sun shiga cikin arangama a birnin Rumbek ... a ranar Juma'a, 9 ga Oktoba, da misalin karfe 4 na asuba. wanda ya haifar da asarar rayuka," in ji ma'aikatar yada labarai ta gwamnatin wucin gadi ta Sudan ta Kudu a cikin wata sanarwa.
Shugaban Ƙasar Salva Kiir ya rusa gwamnati kafin zaɓe a watan Disamba, inda ya bar gwamnati ta wucin gadi.
"A cewar rahotannin jami’an tsaro na farko-farko, an ruwaito cewa an kashe aƙalla mutane 71," ciki har da sojoji huɗu, in ji ma'aikatar.
'An shawo kan lamarin'
Sanarwar ta bayyana cewa an tura ƙarin jami'an tsaro zuwa Rumbek, tana mai cewa yanzu sun "an shawo kan lamarin."
An kama fararen hula huɗu ɗauke da makamai, in ji sanarwar.
Gwamnatin riƙon ƙwarya ta yi Allah wadai da tashin hankalin kuma ta yi kira ga dukkan al'ummomi da su guji ayyukan tashin hankali, su yi taka tsantsan kuma su kwantar da hankalinsu.
Sanarwar ta ƙara da cewa sojoji za su yi ƙoƙarin tabbatar da tsaron fararen hula.

