Sport
Dollar
42,3350
0.2 %Euro
49,1712
0.05 %Gram Gold
5.547,4900
-0.07 %Quarter Gold
9.430,0100
0 %Silver
69,2000
0.51 %Kafa wannan tawaga ya biyo bayan wata ziyarar da wata babbar tawagar Nijeriya karkashin jagorancin Mashawarcin Shugaban Ƙasa kan Tsaro, Nuhu Ribadu, ta kai Washington DC kwanan nan.
Shugaban Nijeriya Bola Tinubu, ya amince da kafa tawagar Nijeriya a Ƙungiyar Aiki na Haɗin Gwiwa kan Tsaro Tsakanin Amurka da Nijeriya (US-Nigeria Joint Working Group), a matsayin wani mataki na ƙarfafa haɗin gwiwa da Amurka wajen magance ƙalubalen tsaro a ƙasar.
Kafa wannan tawaga ya biyo bayan wata ziyarar da wata babbar tawagar Nijeriya karkashin jagorancin Mashawarcin Shugaban Ƙasa kan Tsaro, Nuhu Ribadu, ta kai Washington DC kwanan nan.
Ribadu ne zai jagoranci wannan tawaga ta hukumomi daban-daban, wadda ta haɗa da manyan jami’ai daga manyan cibiyoyin tsaro da na harkokin waje.
Mambobin ƙungiyar aikin, kamar yadda aka ruwaito a cikin sanarwar da mai taimaka wa Shugaban Ƙasa kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya sanya hannu a kai ranar Alhamis, sun haɗa da:
· Ministan Harkokin Waje: Ambasada Yusuf Maitama Tuggar
· Ministan Tsaro: Mohammed Badaru Abubakar
· Ministan Ma’aikatar Cikin Gida: Olubunmi Tunji-Ojo
· Ministan Harkokin Agaji da Kula da Bala’o’i: Bernard M. Doro
· Babban Hafsan Sojoji Janar Olufemi Oluyede
· Babban Darakta na Hukumar Leken Asiri ta Ƙasa: Ambasada Mohammed Mohammed
· Sufeto Janar na 'Yan Sanda Kayode Egbetokun
Sanarwar ta ƙara da cewa, “Malama Idayat Hassan daga Ofishin Mashawarcin Shugaban Ƙasa kan Tsaro (ONSA) da Malam Paul Alabi daga Ofishin Jakadancin Nijeriya a Amurka ne za su zama Sakatariya.”
Shugaba Tinubu ya buƙaci jami’an da su yi aiki tare da takwarorinsu na Amurka don tabbatar da ingantaccen aiwatar da dukkan yarjejeniyoyin tsaro da aka cim ma a lokacin ziyarar.
Ana sa ran Ƙungiyar Aiki na Haɗin Gwiwa Tsakanin Amurka da Nijeriya za ta daidaita dukkanin ƙoƙarin ƙasashen biyu kan yaƙi da ta’addanci da haɗin gwiwar tsaro, da kwanciyar hankali na shiyya.
A cikin 'yan makonnin nan, haɗin gwiwar tsaro ta zama mai matuƙar gaggawa biyo bayan kalamai daga shugaban Amurka.
Kwanan nan, Shugaban Amurka, Donald Trump ya ayyana Nijeriya a matsayin “Ƙasa mai Damuwa ta Musamman” a kan zargin take hakkin 'yancin addini kuma ya yi barazanar ɗaukar matakin soji “idan ba a daina kai hari kan Kiristoci ba.”
Kalaman Trump sun ƙara matsa lamba ga gwamnatin Nijeriya don nuna martani mai ƙarfi ga rashin tsaro.
Comments
No comments Yet
Comment