Sport
Dollar
42,3350
0.2 %Euro
49,1712
0.05 %Gram Gold
5.547,4900
-0.07 %Quarter Gold
9.430,0100
0 %Silver
69,2000
0.51 %Amurka ta dakatar dukkan aikin bai wa ‘yan Afghanistan iznin shiga ƙasar har sai an gama shirye-shiryen nazari kan tsarin tattancewa da na tsaro.
An zargi wani ɗan Afghanistan da laifin harbin dakarun tsaro na West Virginia biyu kusa da Fadar White House a lokacin da kasancewar sojoji a babbar birnin ƙasar da wasu birane ya zama abin tashin hankali.
Daraktan FBI Kash Patelda da kuma Magajin Garin Washington Muriel Bowser sun ce an kai sojojin asibiti kuma suna cikin hali mai muni bayan harbin na ranar Laraba da rana.
Gwamnan Hihar West Virginia, Patrick Morrisey ya janye kalamansa ranar Laraba cewa dakarun sun mutu, yana mai cewa ya samu “rahotanni masu karo da juna” ne game da halin da suke ciki.
Harbin kan sojojin tsaron ƙasar da ba kasafai ake gani a Amurka ba, ana gobe bikin ranar “Miƙa Godiya” yana zuwa ne rikicin da ake a kotu da kuma muhawarar da ake yi kan manufar gwamnatin Trump na amfani da soji wajen yaƙar abin da jami’ai suka bayyana a matsayin matsalar tsaro da ta ƙwace wa al’umma.
Gwamnatin Trump ta yi maza ta ba da umarnin kai sojojin dakarun tsaron ƙasa 500 zuwa Washington.

Wanda ake zargin wanda ya kasance a hannun jami’an tsaro an harbe shi kuma ya ji raunin da ake tunanin ba zai yi barazana ga rayuwarsa ba, in ji wani jami’in tsaro da ba shi zinin magana kan lamarin kuma ya zanta da kamfanin dillancin labaran AP kuma ya nemi a sakaye sunansa.
Wanda ake zargin mai shekara 29, ɗan ƙasar Afghanistan, ya shiga Amurka a shekarar 2021 ta wani shiri mai suna “maraba da ƙawaye”, wani shiri na gwamnatin Biden wanda ya kuɓutar da kuma tsugunar da dubban ‘yan Afghanistan bayan Amurka ta jnaye daga ƙasar, in ji jami’ai.
Shirin ya shigo da kimanin mutum 76,000 ƙasar Amurka, kuma da yawa daga cikinsu sun yi aiki da dakarun Amurka da jami’an duflomasiyya a matsayin tafinta.
Shirin ya fuskanci bincike mai tsanani daga Trump da abokanansa, ‘yan majalisa ‘yan jam’iyyar Republican da wasu hukumomin gwamnati masu sa ido kan giɓi a tsarin tattancewa da kuma saurin shigar mutane duk da cewa cewa masu fafatuka na cewa shirin ya ba da ɗauki ga mutane da ke fuskantar barzanar ramuwar gayya daga Taliban.
Wanda ake zargin, wanda ya kasance yana zama a jihar Washington, jami’an tsaron sun bayyana sunansa a matsayin Rahmanullah Lakanwal, amma har yanzu hukumomi suna ƙoƙarin gano tabbatar da asalinsa, kamar yadda jami’an tsaro biyu da wani mutum da yake da sani game da lamarin suka bayyana.
Mutanen ba su iya tattauna ciakakken bayanin kan binciken da ake kan yi ba kuma sun yi magana da kamfanin dillancin labaran The Associated Press bisa sharaɗi na sakaye sunayensu.
Lakamal ya isa Bellingham, Washington, kimanin kilomita 127 arew ada Seattle, da matarsa da yara biyar, in ji mai gidan da ya zauna a da Kristina Widman.
A ranar Laraba da addare, a cikin wani saƙon bidiyo da ya wallafa a kan shafin sada zumunta, Shugaba Donald Trump ya yi kira da a sake bincike kan dukkan ‘yan gudun hijira ‘yan Afghanistan da suka shiga ƙsar a ƙarƙshin gwamnatin Biden.
“Idan ba za su iya ƙaunar ƙasarmu ba, ba ma son su,” a cewarsa yana mai ƙarawa da cewa harbin “laifi ne kan ƙsar gabaɗaya.”
Jeffery Carroll, wani babban jami’in ‘yan sandan DC, ya ce masu binciken ba su da bayanai game da dalilin harin. Ya ce maharin “ya zo ta kwanan” kuma nan take ya fara harbi kan sojojin, yana mai ishara ga wani bidiyon da masu bincike suka kalla.
“Wannan wani harbi ne na gangan,” in ji Bowser.
Amurka ta dakatar shigar da dukkan ‘yan Afghanistan ƙasar
Ita kuwa hukumar zama ɗan ƙasa da shige da ficen Amurka (USCIS) ta yi shela ranar Laraba cewa ta dakatar da dukkan aiki kan ‘yan Afghanistan.
"Nantake, an dakatar aiki kan duk buƙata ta shiga na ‘yan Afghanistan har sai baba ta gani zuwa ƙarshen binciken tsarin tattancewa,” kamar yadda hukumar ta bayyana kan shafin X.
"Karewa da tsaron ƙsarmu da kuma Amurkawa shi kaɗai muka mayar da hankali a kai ," in ji ta.
Dakarun da aka tura DC ƙarƙashin umarnin ko ta kwana
Trump ya ba da umanin ko ta kwana a watan Aguta kan ƙaddamar da ‘yan sandan tarayya da na jiha da kuma dakarun tsaron ƙasa daga jihohi takwas da kuma gundumar Columbia. Umarnin ya gama aiki bayan wata ɗaya, ama dakarun su ci gaba da kasancewa a wurin.
Kusan dakaru 2,200 ne aka saka cikin dakarun hadin gwiwa da ke aiki a birnin, in ji bayani na bayabayannan da gwamnatin ta fitar.
A makon da ya gabata wani alƙali na tarayya ya ba da umarnin kawo ƙarshen tura dakarun , amma ta kuma saka wa umarninta takunkumi na kwana 21 domin bai wa gwamnatin lokaci na jnaye dakarun ko kuma ɗaukaka ƙara.
Sojojin sun yi sintiri a unguwanni da tashoshin jiragen ƙasa da sauran wasu wurare kuma sun kafa shineg na bincike kan manyan tituna kuma na tura su kwashe shara da kuma gadin wuraren wasanni.
Fiye da sojojin dakarun tsaroin ƙasa 300 na West Virginia ne aka tura a watan Agusta. Kimanin 160 daga cikinsu zaɓi tsawaita aikinsu zuwa ƙarshen shekara , yayin da sauran suka koma gida fiye da makon ɗaya da ya gabata.
Comments
No comments Yet
Comment