Sport
Dollar
42,3350
0.2 %Euro
49,1712
0.05 %Gram Gold
5.547,4900
-0.07 %Quarter Gold
9.430,0100
0 %Silver
69,2000
0.51 %Moscow ta ce Nijeriya tana da 'cikakkiyar kwarewa' wajen magance barazanar tsattsauran ra'ayi, ta yi alƙawarin taimakawa.
Ma'aikatar Harkokin Wajen Rasha ta bayyana a ranar Talata cewa, Rasha a shirye take ta mara wa Najeriya baya a ƙoarinta na yaƙi da ta'addanci, kamar yadda kakakin ma'aikatar Maria Zakharova ta bayyana, inda ta jinjinawa Abuja kan "kokarin da take yi" na yaki da ƙungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi.
Zakharova ta ce matsayar Moscow “ba ta sauya ba,” tana mai nuni da cewa ta’addanci barazana ce ta duniya, ta kuma jaddada shirin Rasha na bayar da taimako tare da hadin gwiwar kasa da kasa, da hukumomin Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Afirka.
"Rasha a shirye take ta ci gaba da samar da duk wani taimako da ya dace ga abokan hulɗarta na Najeriya," in ji ta, inda ta ƙara da cewa sojojin Najeriya da hukumomin tsaro suna "cikakkiyar gogewa wajen tinkarar barazanar ta'addanci yadda ya kamata."
Ta jaddada cewa fararen hula, ciki har da mata da yara, na ci gaba da shan wahala sosai sakamakon hare-hare, haka su ma jami'an gwamnati da na tsaro.
Nijeriya na fuskantar tashin hankali daga ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai ciki har da Boko Haram, wadda ta fara tarzoma tun daga shekarar 2002 daga Jihar Borno kuma har yanzu tana ci gaba da kai hare-hare a duk da gagarumar kassara ta da sojojin Najeriya suka yi a shekarar 2015.
Sabbin hare-hare kan makarantu ya sa hukumomi rufe makarantu a jihohi da dama, yayin da Shugaba Bola Tinubu ya soke tafiyar da ya shirya zuwa Afirka ta Kudu don taron G20 a farkon wannan watan saboda karuwar matsalolin tsaro.
Comments
No comments Yet
Comment