Dollar

42,3350

0.2 %

Euro

49,1712

0.05 %

Gram Gold

5.547,4900

-0.07 %

Quarter Gold

9.430,0100

0 %

Silver

69,2000

0.51 %

Bayanai na cewa an kuɓutar da 'yan matan ne da safiyar Talata ta hanyar tattaunawa, kuma tuni suka ƙarasa birnin Kebbi, babban birnin jihar a cikin daren Talata, kamar yadda Kwamishinan Labarai Jihar Yakubu Ahmed BK ya shaida wa TRT Afirka.

An sako 'yan matan makarantar sakandaren Jihar Kebbi 24 da 'yan bindiga suka sace

An sako 'yan matan makarantar sakandaren Jihar Kebbi da 'yan bindiga suka sace a daren Litin ta makon jiya, a cewar hukumomi.

Kwamishinan watsa labaran jihar Yakubu Ahmed BK ya tabbatar wa TRT Afirka lamarin, inda ya ce tuni ɗaliban suka isa Birnin Kebbi “kuma dukkaninsu su 24 suna cikin ƙoshin lafiya”.

Wasu kafofin watsa labaran ƙasar na cewa an kuɓutar da ‘yan matan ne sakamakon wani yunƙuri da Ofishin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaro da haɗin gwiwar Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS suka yi, ba tare da zubar da jini ba.

Fadar shugaban ƙasar ta fitar da sanarwa ɗauke da sa hannun kakakin fadar Bayo Onanuga a yammacin Talata, inda ta ce Shugaba Tinubu ya yi farin cikin da sakin ‘yan matan, sannan ya yi kira ga jami’an tsaro su ƙara ƙaimi wajen kuɓutar da sauran duk wadanda suke hannun masu garkuwa da mutane.

“Na samu nutsuwa cewa duka ‘yan matan 24 suna hannu yanzu,” a cewar Shugaba Tinubu, kamar yadda sanarwar ta ambato.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#