Dollar

42,3350

0.2 %

Euro

49,1712

0.05 %

Gram Gold

5.547,4900

-0.07 %

Quarter Gold

9.430,0100

0 %

Silver

69,2000

0.51 %

Marigayi Sheikh Dahiru Bauchi ya rasu ne da asubahin ranar Alhamis 27 ga watan Nuwamba bayan fata da jinya da ya yi, ya bar gado mai yawa na ilimi, mabiya, da tasiri a fagen addini da zamantakewa a Nijeriya.

Tarihin rayuwar marigayi Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi da gudunmawarsa ga addinin musulunci

Sheikh Dahiru Usman Bauchi (OFR) ya kasance ɗaya daga cikin manyan malamai kuma jagororin addinin Musulunci a tarihin Nijeriya da yankin Afirka ta Yamma a ƙarni na 20 da na 2, ya jagoranci mabiyan Dariƙar Tijjaniyya da yawa kuma ya yi tasiri a fannin Tafsirin Al-Qur'ani da wa'azi.

An haife malamin a yankin Konkiyel da ke karamar hukumar Darazo na jihar Bauchi a Nijeriya, a ranar 29 ga watan Yunin 1927, wanda ya yi daidai da 1 ga watan Muharram na 1346H.  

Asalin Bafulatace ne, wanda tsatsonsa na uwa suka fito daga karamar hukumar Nafada na Jihar Gombe a yankin Arewa maso gabashin Nijeriya .

Tafarkin Ilimi (Qur'ani da Karatun Addini)

Sheikh Dahiru Bauchi ya fara neman ilimi tun yana ƙarami, kuma ya yi zurfi wajen sanin addini. Ya fara karatun Kur’ani ne a wajen mahaifinsa, Alhaji Usman, wanda shi ma fitaccen malami ne.

Ya nuna hazaka ta musamman inda ya haddace dukkanin Al-Qur'ani mai tsarki tun yana yaro a karkashin kulawar mahaifinsam sannan ya yi karatu a wajen manyan malamai waɗanda suka yi fice a fannoni daban-daban na addini da suka haɗa da Fiqhu (Ilimin Shari'a), Tauhidi, da Hadisi.

Karkashin koyarwar Sheikh Tijjani Usman Zangon-Bare-bari da Sheikh Abubakar Atiku
da kuma Sheikh Abdulqadir Zaria.

Dariƙar Tijjaniyya

Ana ɗaukar shi a matsayin Babban Jagoran Dariƙar Tijjaniyya a Nijeriya kuma ya kasance mamba na Kwamitin Shugabannin Tijjaniyya na Duniya.

Mahaifinsa muqaddam ne a Dariƙar Tijjaniyya, kuma Sheikh Dahiru ya gaji wannan matsayi da kuma hanyar Addini, inda ya zama babban malami mai yaɗa koyarwar Shehu Ahmad Tijjani. Sheikh Dahiru Bauchi ya kasance ba kawai malami ba ne, har ma jagora a matakin ƙasa da na duniya.

Ya kasance memba kuma mataimakin shugaban kwamitin bayar da fatawa na Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Nijeriya, wanda ke nuna matsayinsa na jagora a harkar shari'a da ra'ayin addini.

Shahararsa da Tasirinsa

Abin da ya fi sa Sheikh Dahiru Bauchi ya shahara shi ne salo da yawan tafsirinsa.
Ya yi fice wajen fassarar Al-Qur’ani mai tsarki da harshen Hausa, musamman a cikin watan Ramadan.

Ana kiransa da sunan “Tafsir Sheikh Dahiru Bauchi”, wanda ya shahara matuƙa kuma aka fi yadawa a rediyo, Talabijin, da kuma kafofin sada zumunta a Arewacin Nijeriya.

Ya shahara da yawon wa’azi a jihohi daban-daban na Nijeriya da ƙasashen waje, inda yake mai da hankali kan koyarwar Tauhidi, Shari'a, ɗorewar ɗabi'a mai kyau, da kiran zaman lafiya.

Dangantaka da Shehu Ibrahim Inyass

Dangantakarsa da gidan Shehu Ibrahim Niasse na Kaolack, Senegal, ta ƙara ƙarfafa matsayinsa a matsayin jagoran Tijjaniyya na Afirka ta Yamma.
Ya kasance babban mabiyi kuma masoyin Sheikh Ibrahim Niasse, wanda aka fi sani da Kaolack.

Ya ƙarfafa dangantakar sa da gidan Shehu Niasse ta hanyar aure; an ruwaito ya auri ɗiyar Sheikh Ibrahim Niasse, inda aka ɗaura auren a masallacin Shehu Niasse da ke Senegal.

 
 Tsawon Rai da Iyali

Ya kasance mai tsawon rai, inda ya shiga shekaru kusan 100. Ya bayyana a cikin wata hira cewa Allah ya hore masa 'ya'ya masu yawa, waɗanda aka ƙiyasta tsakanin 60 zuwa 70, da kuma jikoki masu yawa, wanda ke nuna yadda Allah ya albarkaci rayuwarsa.

A shekarar 2014, ya tsira daga wani mummunan harin bam da aka kai kan ayarinsa a Kaduna, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama. Wannan ya nuna haɗarin da ya fuskanta a kan hanyar da'awarsa.

 An bashi lambar girmamawa ta Officer of the Order of the Federal Republic (OFR) a Najeriya.

Marigayi Sheikh Dahiru Bauchi ya rasu ne da asubahin Alhamis 27 ga watan Nuwamba bayan fata da jinya da ya yi, ya bar gado mai yawa na ilimi, mabiya, da tasiri a fagen addini da zamantakewa a Nijeriya.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#