Yaƙin Isra'ila a Gaza ya shiga rana ta 355, inda ta kashe kusan Falasɗinawa 41,495 – yawacinsu mata da yara – tare da jikkata kusan 96,006 kuma wani ƙiyasi ya nuna cewa fiye da mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzan gine-ginen da aka rusa.
Laraba, 25 ga Satumban 2024
1404 GMT — Akalla mutum 51 ne suka mutu sannan wasu 223 suka jikkata sakamakon sabbin hare-haren da Isra’ila ta kai kan kasar Lebanon, in ji Ministan Lafiya na Lebanon Firass Abiad yayin wani taron manema labarai.
1410 GMT — Mutum 90,000 sun rasa matsugunansu a Lebanon tun ranar Litinin: MDD
Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin mutum 90,000 ne suka rasa matsugunansu a Lebanon cikin wannan mako, yayin da Isra'ila ke kai hare-hare kan wuraren da ta ce na kungiyar Hezbollah ne a fadin kasar, sannan kuma kungiyar ta Lebanon ta kai hari kan Isra'ila.
Tun daga ranar Litinin, Hukumar Kula da Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta rubuta "sabbin mutane 90,530 da suka rasa matsugunansu", in ji wata sanarwa.
Daga cikin su, "da yawa daga cikin mutane sama da 111,000 da suka rasa matsugunansu ne tun watan Oktoba... na iya zama sun sake rasa matsugunan nasu a karo na biyu", in ji wata sanarwa da ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar, tana mai nuni da fara rikicin kan iyakokin kasar tsakanin Isra'ila da Hezbollah.
