Sport
Dollar
40,9411
0.09 %Euro
47,9607
0.44 %Gram Gold
4.383,8900
0.13 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Ɓangarorin sun rattaba hannu kan wata sanarwa ta haɗin gwiwa game da tattaunawa da yarjejeniya tsakanin ma’aikatar tsaron Rasha da ma’aikatun tsaron ƙasashen AES
Ministan Tsaron Rasha Andrey Belousov ya karɓi baƙuncin tattaunawa da takwarorinsa daga ƙasashen ƙungiyar haɗin kan ƙasashen yankin Sahel (AES) kuma ya bayyana cewa a shirye ƙasarsa take ta ba da tallafi domin tabbatar tsaro a yankin.
“Matakin kafa haɗaka ya samo asali ne daga zaɓin da mutane yankin Sahel suka yi da raɗin kansu, wata hanyar ci-gaba cikin lafiya mai ɗorewa,” kamar yadda ma’aikatar tsaron Rasha ta ambato Belousov na cewa ranar Alhamis.
Belousov ya ce ya bayyana cewa a shirye Rasha take domin ba da cikakken taimako kan tabbatar da zaman lafiya a yankin, yana mai ƙarawa da cewa Moscow na goyon bayan matsayar AES kan “buƙatar ƙarfafa tsaro da kare ƙasashe da kuma ‘yancin kai.”
Comments
No comments Yet
Comment