Dollar

40,9411

0.09 %

Euro

47,9607

0.44 %

Gram Gold

4.383,8900

0.13 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Kamfanin dillancin labaran Nijar(ANP) ya ambato wata sanarwar da ministan shari’ar ƙasar, Alio Daouda, ya fitar tana cewa an yi ammanar cewa ƙungiyoyin ƙwadagon huɗu ba sa aiki domin inganta aikin ɓangaren shari’a domin kare muradun al’umma.

Ma’aikatar Shari’ar Nijar ta yi bayani game da rushe ƙungiyoyin ƙwadago

Ma’aikatar Shari’ar Jamhuriyar Nijar ta yi bayani game da matakin da gwamnatin ƙasar ta ɗauka na rusa ƙungiyoyin ƙwadago huɗu da ke fannin shari’a.

Kamfanin dillancin labaran ƙasar, (ANP) ya ambato wata sanarwar da Ministan Shari’ar ƙasar, Alio Daouda ya fitar tana cewa an yi amannar cewa ƙungiyoyin ƙwadagon huɗu ba sa aiki domin inganta aikin ɓangaren shari’a domin kare muradun al’umma.

Ƙungiyoyin ƙwadagon sun haɗa da ƙungiyoyin SAMAN da SNAJ da SYNCAT da kuma UMAN.

Sanarwar ta ƙara da cewa maimakon ƙoƙarin kare muradun al’umma, ƙungiyoyin na aikin kare muradun kansu ne, lamarin ke ƙasa-ƙasa da harkar yi wa ƙasa hidima.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#