Sport
Dollar
40,9411
0.09 %Euro
47,9607
0.44 %Gram Gold
4.383,8900
0.13 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Amma masu sharhi sun ce duk da iƙirarin na Arne Slot, jadawalin nuna ɗa’a yayin wasa na kakar bara bai nuna Liverpool na kangaba a wajen nuna gaskiya ba.
Kocin Liverpool, Arne Slot ya yi iƙirarin cewa ƙungiyarsa ce mafi nuna gaskiya a gasar Firimiya ta Ingila.
Rahotannin sun ambato Slot na cewa, "Idan akwai kungiya ɗaya a [Firimiya] lig da a ra’ayina ita ce mafi gaskiya yayin wasa..., kuma wadda ‘yan wasanta ba sa taɓa yin langwai kuma ba sa taɓa jan lokaci da sauran shegantaka, to mu ne [Liverpool]”.
Slot ya ce ya yi imanin ‘yan wasansa suna da gaskiya saboda ba sa faɗuwa ba tare da dalili ba, sai idan an musu ƙeta.
Kocin ya ce wani lokacin ‘yan wasan nasa sukan nuna gaskiya da yawa, har ba sa ribatar lokacin da aka musu ƙeta, don samun bugu ko don a hukunta abokan adawarsu.
Ya ba da misali da wasan kofin Community Shield da Liverpool ta kara da Crystal Palace, inda aka riƙe Florian Wirtz, amma bai faɗi ƙasa ba.
Comments
No comments Yet
Comment