Sport
Dollar
40,9411
0.09 %Euro
47,9607
0.44 %Gram Gold
4.383,8900
0.13 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Umarnin gwamnatin na zuwa ne bayan hatsarin helikwafta ya kashe jami’ai takwas, inda ake iƙirarin cewa wasu limaman addinin Kirista sun bayyana cewa lamarin zai auku kafin hatsarin.
Ofishin Shugaban Ƙasar Ghana ya ba da umarni ga shugabannin addini su dinga miƙa ‘saƙonnin ikirarin wahayi masu muhimmanci ga ƙasa’ domin a tantance su a hukumance.
An ɗauki matakin ne domin aiki kan gargaɗi na ruhi mai alaƙa da manyan shugabanni da aikin gwamnati da tsaron ƙasa da kuma zaman lafiyar al’umma, in ji wata sanarwa daga ofishin kula da addinai na fadar shugaban ƙasar, kamar yadda kamfanin dillacin labaran ƙasar ya ruwaito ranar Lahadi.
Umarnin yana zuwa ne bayan wani hoton bidiyo ya yi ta yawo a shafukan sada zumunta inda wasu limaman Kiristoci ke iƙirarin cewa sun ga hatsarin helikwaftan da ya kashe jami’an gwamnatin kafin ya auku.
Hatsarin helikwaftan ya auku ne ranar 6 ga watan Agusta na shekarar 2025, a lokacin da wani jirgin soji mai ɗauke da jami’an gwamnati ya faɗi, lamarin da ya sa jami’an gwamnati bakwai suka rasa rayukansu.
Jana’izar waɗanda lamarin ya shafa
Waɗanda lamarin ya rutsa da su sun haɗa da Ministan Tsaro Edward Omane Boamah da Ibrahim Murtala Mohammed, tsohon ministan muhalli da kimiyya da fasaha.
Comments
No comments Yet
Comment