Sport
Dollar
38,8155
0.01 %Euro
43,4855
-0.02 %Gram Gold
4.056,7400
0.08 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Bayan nuna bajintar cin ƙwallaye a gasar gida ta Faransa da gasar Zakarun Turai, Ousmane Dembele ya jagoranci PSG wajen lashe kofin Ligue 1 da na French Super Cup.
Zakaran ƙwallon ƙafa na Paris Saint-Germain ta Faransa, kuma ɗan takarar kyautar Ballon d'Or ta bana, Ousmane Dembele ya zama gwarzon shekara na gasar Ligue 1.
Dembele ya samu tagomashi matuƙa a kakar bana, inda yake kangaba wajen cin ƙwallaye a gasar, kuma ƙungiyarsa ta kama hanyar cin zunzurutun kofuna huɗu a kakar bana.
PSG ta fito wasan ƙarshe na gasar Zakarun Turai, wadda za a buga ƙarshen watan Mayu. Gabanin nan za ta buga wasan ƙarshe na gasar French Cup ranar 24 ga Mayu.
A bikin ba da kyautukan bajinta na ƙarshen kaka na UNFP da aka yi a birnin Paris a maraicen Lahadi, PSG ce ta samu rinjayen lashe kyautuka har 14.
Dembele haziƙin ɗan wasa ne da tauraruwarsa ke haskawa, kuma ya zo PSG ne daga Barcelona a 2023.
Ƙaruwar tagomashi
A kakarsa ta farko bara, da kuma a rabin kakar bana, Dembele bai taka rawar gani a tawagar da kocin Luis Enrique ke jagoranta ba.
Amma zuwa yanzu ya ci ƙwallaye 33 da tallafin ƙwallo 13 cikin wasanni 46 a duka gasanni, wanda ke nufin yana cin ƙwallo duk minti 67.
Wannan ƙoƙari da yake nunawa ya taimaka wa PSG samun fifiko a duka gasanni, inda ta ci kofin French Super Cup, da kuma gasar Ligue 1 da gagarumar tazara.
A yanzu dai PSG za ta kara da Reims don neman lashe kofin French Cup, sannan ta kara da Inter Milan don neman ɗaga kofin Zakarun Turai.
Lashe kofunan biyu zai bai wa PSG damar kammala ɗaukar kofuna hudu rigis, don kafa tarihin bajinta a Faransa da ma duniyar ƙwallo.
Comments
No comments Yet
Comment