An wallafa jawabin Shugaba Erdogan na UNGA-81 a matsayin littafi cikin harsuna uku
Littafin ya tattaro saƙonnin shugaban ƙasar Turkiyya game da kisan ƙare-dangi a Gaza da rikice-rikicen duniya da kuma garambawul ga tsarin dokokin duniya, mai taken "Yiwuwar Samun Duniya Mai Adalci."
24 Satumba 2026
Shugaban Turkiyya Erdogan ya buƙaci haɗin ƙan Musulmai, ya soki nuna wariya
Erdogan ya ce al'ummomi masu ƙarfi da haɗin kai za su iya taimakawa wajen yaƙi da ƙiyayya da tsangwama da kuma nuna wariya ga al’ummar Musulmai.
24 Satumba 2026
Iran ta yi tayin sake buɗe Mashigar Hormuz cikin kwanaki bakwai idan Amurka ta sassauta matsin lamba
Kamfanin dillanacin labarai na Turkiyya, Anadolu ya ce bai iya tabbatar da sahihancin wannan batu ba da kansa.
22 Satumba 2026
Shugaba Erdogan na Turkiyya ya tafi New York taron Majalisar Dinkin Duniya
Kusan shugabannin ƙasashe 130 ne za su halarci taron, a daidai lokacin da tsarin duniya da aka kafa bayan Yaƙin Duniya na Biyu ke fuskantar barazana, yayin da ita kanta Majalisar Ɗinkin Duniya ke fama da ƙalubale.
20 Satumba 2026
'Turkiyya za ta duba buƙatun Saudiyya ƙarƙashin yarjejeniyar Makkah yayin da Houthi ke kai hari'
Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Hakan Fidan, ya ce akwai yiwuwar Saudiyya na da wasu buƙatun soji sakamakon hare-haren baya-bayan nan da ’yan Houthi suka kai, kuma Turkiyya za ta duba waɗannan buƙatu ƙarƙashin yarjejen
20 Satumba 2026
Yarjejeniyar Makka na aike wa da 'Saƙon haɗin kai da zaman lafiya': Firaministan Pakistan
Shehbaz Sharif ya ce Yarjejeniyar Hadin Gwiwa ta Makka ta kusanto da Pakistan, Saudiyya da Turkiyya ga juna, a yayin da Bangaladash ke duba yiwuwar shiga yarjejeniyar.
28 Agusta 2026
An haƙo wani sassaƙen ɗan'adam zaune a kan damisa mai shekaru 11,000 a Turkiyya
Wani sassaƙe da aka gano a Karahantepe, kusa da Gobeklitepe, na bayar da sabbin bayanai game da addini, tsarin idaba da zamantakewar al’ummun Neolithic da ke kudu maso-gabashin Turkiyya.
25 Agusta 2026
Turkiyya ta ƙara haɓaka kasuwancin da take yi da ƙasashen Musulmi
Kayayyakin da Turkiyya ta fitar zuwa ƙasashen Musulmi ya kai dala biliyan 41.5 a cikin watanni bakwai na farkon shekarar 2026, bayan da ya ƙaru da dala miliyan 345.7.
24 Agusta 2026
Tsohon Ministan Tsaron Isra'ila Yaalon ya zargi Netanyahu da neman rikici da Turkiyya
Moshe Yaalon ya ce Netanyahu na rura wutar rikici da Turkiyya da gangan ta hanyar kai hari kan wani sansanin jiragen sama da ke arewacin Syria, inda ya zargi Firaministan da tsawaita rikice-rikice domin guje wa shari’a.
20 Agusta 2026
Aselsan: Kamfanin tsaro na Turkiyya zai baje-kolin jirgin ƙarƙashin ruwansa a bikin Teknofest
Jirgin na da ƙwarewar da zai iya aiki da kansa ta hanyar sa ido da binciken ƙwaƙƙwaf a wurare masu haɗari ko kuma masu wahalar isa a ƙarƙashin ruwa, ba tare da ya samu taimako mai ƙarfi daga bil’adama ba.
20 Agusta 2026
Trump ya yi 'murna' kan yarjejeniyar tsaro ta Makka da Turkiyya da Pakistan da kuma Saudiyya suka yi
Shugaban Amurka ya yaba da yarjejeniyar a matsayin babban mataki na farko da zai kai ga haɗin gwiwa tsakanin yankuna da ƙarfafa tsaro a yankin Gabas ta Tsakiya, yana mai taya shugabannin ƙasashen uku murna.
17 Agusta 2026
Shugaba Erdogan ya jinjina wa shekara 25 na Jam'iyyar AK kan samar da 'sauyi mai tarihi' a Turkiyya
Yayin da jam’iyyar AK ta cika shekaru 25, Erdogan ya ce an kafa ta ne a ranar 14 ga Agustan 2001, da nufin sake fasalin makomar Turkiyya, ƙarfafa alaƙar da ke tsakanin gwamnati da ’yan ƙasa, da tabbatar da cewa ƙasar za
14 Agusta 2026
Turkiyya ta kama mutum 30 a wani samame da aka kai kan ƙungiyar masu aikata laifuka ta Alihan
A cewar rahoton Hukumar Binciken Laifukan Kuɗi ta Turkiyya (MASAK), yawan hada-hadar kuɗi na kamfanoni da dama da ke da alaƙa da ƙungiyar ya ƙaru sosai bayan shekarar 2020, yayin da aka rarraba wasu kamfanonin tare da ca
13 Agusta 2026
Turkiyya za ta ci gaba da taka rawa da kuma shiga tsakani a Libya, in ji Ministan Harkokin Waje
Turkiyya tana goyon bayan sulhu tsakanin yankin gabas da na yammacin Libya, a cewar Fidan a yayin da Ankara take ƙarfafa hanyar tattaunawa da zaman lafiya da haɗin a ƙasar.
13 Agusta 2026
Cikin hotuna: Turkiyya ta haskaka muhimman wurare don murnar Yajejeniyar Tsaron Hadin Gwiwa ta Makka
Sabuwar yarjejeniyar tsaro ta Turkiya, Saudiyya da Pakistan ta zama abubuwan ɗaukar hankali a Ankara da Istanbul, inda aka haskaka muhimman gine-gine don nuna saƙon goyon baya da tsara makoma mai muhimmanci.
10 Agusta 2026
Hari kan ɗaya daga cikinmu tamkar a kan dukanmu ne, in ji Turkiyya, Saudiyya da Pakistan
Turkiyya, Saudiyya da Pakistan sun saka hannu kan wata yarjejeniya ta tsaro a birnin Makka inda a karkashin yarjejeniyar, duk wani hari da aka kai wa ɗaya daga cikin ƙasashen uku za a ɗauke shi a matsayin hari da aka kai
7 Agusta 2026
Mohamed Salah ya sanya hannu kan kwantiragin shekaru biyu da Trabzonspor ta Turkiyya
Tauraron, ɗan ƙasar Masar zai riƙa karɓar albashin sama da dala miliyan 11.5 a kowace shekara da garaɓasar dala miliyan 8 a kowace kakar wasa.
6 Agusta 2026
Turkiyya ta kama ɗanta'addan FETO da ake nema bisa ƙoƙarin kashe Shugaba Erdogan a shekarar 2016
Wanda ake zargin, wani keftin na soji da aka kora kuma tsohon matuƙin helikwafta, ya kasance ana nemansa ruwa-a-jallo a ƙarƙashin wata Jar Sanarwar ta Hukumar 'Yansandan Duniya.
1 Agusta 2026
Turkiyya ta yi fice a Gasar Duniya ta Rubutu a Kwamfuta da kambi 36
Masu gogayya daga kasashe 34 sun gwada saurin rubutu da rashin kuskure a wajen Gasar Rubutu a Kwamfuta ta Duniya ta Intersteno da ke gudana a Liverpool.
31 Yuli 2026
Turkiyya da Nijeriya sun ƙara ƙarfafa daɗin gwiwa kan ƙera jiragen ruwa
Gwamnatin Nijeriya na son kamfanonin ƙera jiragen ruwa na Turkiyya su zama abokan hulɗa na dindindin wajen haɓaka ƙarfin ƙasar na ƙera jiragen ruwa a cikin gida.
29 Yuli 2026
Ayyukan ‘yan kama-wuri-zauna na Isra’ila na barazana ga ƙoƙarin zaman lafiya a Ƙudus: Turkiyya
"Ankara za ta ci gaba da kare haƙƙin al'ummar Falasɗinu da na birnin Kudus a ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa," in ji Shugaban hukumar Sadarwa na Turkiyya.
24 Yuli 2026
Turkiyya ta yi kira ga Amurka da Iran su koma kan yarjejeniya, su kuma yi aiki tare da Qatar
Babban jami'in diflomasiyyar Turkiyya ya ce Doha tana amfani da dukkan hanyoyin diflomasiyya don magance rikici tsakanin Amurka da Iran tare da fatan samun ci gaba mai kyau a cikin kwanaki masu zuwa.
20 Yuli 2026
Girgizar ƙasa mai maki 5 ta girgiza gabashin Turkiyya
Girgizar ƙasar ta afka wa gundumar Battalgazi a wani wuri mai zurfi na kilomita 15.59, in ji hukumar bada agajin gaggawa ta Turkiyya.
18 Yuli 2026
Netanyahu ya fusata Trump bayan ya caccaki shirin Amurka na sayar wa Turkiyya F-35: Rahoto
Rahoton, wanda ya ambato jami'an Fadar White House guda biyu, ya ce Trump ya fusata matuƙa bayan Netanyahu ya soki yiwuwar sayar da jiragen a wata hira da ya yi da Fox News, jim kaɗan kafin shugaban Amurka ya tafi Ankara
17 Yuli 2026