Turkiyya ta bayyana cewa ta “matukar shiga cikin jimami” sakamakon hatsarin jirgin soji da ya faru a Jihar Ondo ta Nijeriya.
Turkiyya ta bayyana cewa ta “matukar shiga cikin jimami” sakamakon hatsarin jirgin soji da ya faru a Jihar Ondo ta Nijeriya.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta ce a cikin wata sanarwa: “Mun matukar shiga cikin jimami sakamakon asarar rayuka da hatsarin jirgin soji ya jawo a yau a Jihar Ondo ta Nijeriya.”
Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ranar Litinin ta kuma miƙa ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a hatsarin da kuma al’ummar Nijeriya.
Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya ayyana kwanaki uku na zaman makoki ranar Talata tare da bayar da umarnin gudanar da bincike kan hatsarin.
Ministan Sufurin Jiragen Sama na Nijeriya, Festus Keyamo ya shaida wa manema labarai cewa jirgin ya faɗo ne kusa da sansanin sojin ruwa na Igbokoda.
Ya ce mutum 25 da ma’aikatan jirgin bakwai ne ke cikin jirgin, inda ya ƙara da cewa an gano tarkacen jirgin, kuma ana ci gaba da gudanar da ayyukan ceto da bincike a yankin.
Keyamo ya ce jirgin ATR-42 na Rundunar Sojin Saman Nijeriya yana kan hanyarsa daga Benin zuwa Legas.
Daga bisani, Rundunar Sojin Saman Nijeriya ta sake bayyana adadin waɗanda suka mutu zuwa 25, inda ta ce fasinjoji 20 da ma’aikatan jirgin biyar ne ke cikin jirgin, kuma babu wanda ya tsira.
Rundunar ta ce jirgin na gudanar da wani aiki na yau da kullum ne a lokacin da hatsarin ya faru.

