Babban jami'in na MƊD ya ce ƙoƙarin Turkiyya ya "matuƙar ƙayatar" da shi.
Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD) Antonio Guterres ya yaba wa yadda Turkiyya ta tsara taron Sauyin Yanayi na COP31 ranar Talata a birnin Bahar Rum na Antalya na Turkiyya.
“Na halarci tarukan COP da yawa, kuma ingancin yadda Turkiyya ta shiya wannan COP ɗin ya ƙayatar da ni,” kamar yadda Guterres ya shaida wa Anadolu game da taron yanayi na shekara-shekara, wanda aka fara yi ranar Litinin kuma za a yi har zuwa ranar 20 Nuwamba.
Kalaman Guterres sun biyo bayan yabo daga Dana Gunders ranar Litinin, shugabar ƙungiyar sa-kai ta Amurka ReFED, wadda ta yaba wa ƙoƙarin Turkiyya na haɗa kan ƙasashe waje magance matsalar lalata abinci.
Gunders ta bayyana tsarin Turkiyya na Kawar Da Shara da rawan da Maiɗakin Shugaban Ƙasa wajen jan hankalin duniya zuwa kan lamarin.
“Ta hanyar COP da kuma Gidauniyar Shirin Kawar da Shara, Turkiyya tana nuna shugabanci mai ƙarfi,” in ji ta, tana mai ishara ga Taron Kawar da Shara na shekra-shekara, wanda ke tara mahalarta daga sassan duniya.
Ta kuma ce maiɗakin Shugaba Erdogan ta taimaka wajen jan hankalin ƙasashen duniya zuwa ga lalata abinci.
“Ina tunanin hankali ya koma kan wannan batu sosai bisa taimakon Maiɗakin Shugaban Ƙasa,” in ji ta.
TRT Afrika — TRT Afrika
Hoto: Anadolu Ajansı

