Duran ya yi watsi da wata duniyar dijital inda aka fi jin wasu muryoyi fiye da wasu.
Shugaban ofishin sadarwar Turkiyya, Burhanettin Duran, ya ce ba za a yarda wasu ‘yan tsirarun manyan kamfanonin fasaha su tsara abin da biliyoyin mutane za su rinƙa gani a shafukan sada zumunta ba.
“Dole duniyar dijital ta yau ta ɗauki tare da aiki da ƙa’ijoji uku: fayyace gaskiya da adalci a wajen bayyana bayanan algorizin da kuma tabbatar da bambance-bambance,” kamar yadda Duran ya bayyana a wani zaman taron TRT World Forum mai taken "Wane ne ke da iko a Lokacin Algorizin? kamfanoni da ƙasashe ‘yan ƙasa,” ranar Asabar.
Duran ya ce kamfanonin fasaha ba za su iya kasance suna da tasiri mai yawa kan rayuwar mutane ba, ba tare da kasancewa suna amsa tambayoyi game da makatan da suke ɗauka ba.
“Kamfanonin Fasaha ba za su iya kasancewa masu tasiri da yawa a kan rayuwar mutanen ba ba tare da ana musu tambayoyi game da matakan da suke ɗauka ba,” in ji shi.
Ya kuma yi watsi da wata duniyar dijital inda aka fi jin wasu muryoyi fiye da wasu.
“Ba za mu iya amanna da duniyar dijital inda wasu muryoyi ke kai ga miliyoyin mutane ba yayin da da ƙyar ake jin wasu,” in ji Duran.
“Dole duniya mai adalci ta yi tunani game da bambance-bambancen duniyar kanta,” kamar yadda ya bayyana.
“Babu wata ƙasa ɗaya ko al’ada ɗaya ko kuma kamfani ɗaya da ya kamata ya mamaye ta.”
An fara taron TRT World Forum na 10 ne Istanbul ranar Jumma’a a ƙarƙashin taken "Wata Duniya Da Ba ta da Cibiya: Wa Zai yi Jagoranci A Lokacin da Dokokin Suka ƙare?"
Taron da Kafar Watsa Labaran Turkiyya TRT Ke shiryawa a ko wace shekara tun shekarar 2017, wanda ya tara manyan mutane a ɗakin taron Istanbul Congress Centre ya haɗa ‘yansiyasa da malamai da ‘yanjarida da masu wasan motsa jiki da masu zane da wakilan ƙungiyoyi masu zaman kansu domin magance matsalolin duniya.
Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya gabatar da jawabai na buɗe taron a rana ta farko ta taron ranar Jumma’a, tare da Daraktan Ofishin Sadarwa Shugaban Ƙasa Burhanettin Duran da kuma Darakta Janar na TRT Mehmed Zahid Sobaci.
TRT Afrika — TRT Afrika
Hoto: AA

