Matar ƙanin Muhammadu Sani ce kawai ta tsira in ji rahotanni, yayin da sauran mutum 12 da ke cikin gidan sun mutu sakamakon tsananin zafi da wuta.

'Yanbindiga sun ƙone mutum 12 'yan gida ɗaya a Jihar Zamfara ta Nijeriya

Ɓarayin daji sun kashe mutum goma sha biyu ‘yan gida ɗaya bayan sun cinna wa gidansu wuta a wani harin da suka kai wani ƙauye a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Nijeriya, kamar yadda kafafan watsa labaran ƙasar suka ruwaito.

Kafafan watsa labaran ƙasar da suka haɗa da Daily Trust da The Punch da Premium Times da kuma Vanguard sun ba da rahoton cewa lamarin ya auku ne a ƙauyen Gidan Taba da ke ƙaramar hukumar Maradun na jihar Zamfara ranar Asabar da dare.

Rahotanni sun ƙara da cewa an sace wasu mutum bakwai a harin.

Mazauna ƙauyen sun ce maharan sun far ma gidan wani da ake kira Mallam Muhammadu Sani ne da misalin ƙarfe 10 na dare.

Mutum goma sha uku daga cikin gidan Muhammadu Sani, ciki har da matansa biyu da ‘ya’ya shida tare da matar ƙaninsa da ‘ya’yansu uku ne suka maƙale a cikin wani ɗaki bayan sun rufe kansu a ciki domin kuɓuce wa maharan don kada su yi garkuwa da su.

‘Yan bindigar sun umarci waɗanda suke cikin ɗakin su buɗe ƙofa, amma da suka ƙi, sai suka cinna wa ɗakin wuta, in ji mazanuna ƙaunyen.

Matar ƙanin Muhammadu Sani ce kawai ta tsira, in ji rahotanni, yayin da sauran mutum 12 da ke ciki suka mutu sakamakon tsananin zafi da wuta.

Kwamishinan ‘yansandan jihar Zamfara ya tabbatar da harin, amma ya ce adadin waɗanda suka mutu 11 ne, in ji jaridar Daily Trust.

Daga baya dai an bunne ‘yan gida ɗayan a ranar Lahadi, in ji rahotanni.

Harin na Gidan Taba shi ne na baya bayan nan a cikin jerin hare-hare a ƙaramar hukumar Maradun na jihar Zamfara.

A makon da ya gabata, ‘yan bindiga sun yi wa jami’an tsaro kwanton ɓauna a Gidan Kano a kan babbar hanyar Gusau zuwa Sokoto.

Jami’an na tafiya ne a cikin wata motar bas mai ɗaukar mutum 18 ta hukumar sufuri ta jihar Zamfara domin samar da tsaro a lokacin sake zaɓen fid da gwani na jam’iyyar APC a mazaɓar Zamfara ta Arewa. Jami’ai biyar aka kashe a kwanton ɓaunar.

TRT Afrika — TRT Afrika

#