Sport
Dollar
41,3314
-0.08 %Euro
48,5942
0.03 %Gram Gold
4.836,6100
-0.19 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Motar ta faɗa cikin a kogin ne a lokacin da take yunƙurin tsallake wata gada da ta karye wadda ke tsakanin ƙauyen Gwalli da garin Gummi a Jihar Zamfara.
Fasinjoji 19 sun rasa rayukansu a ranar Asabar a lokacin da wata motar haya ɗauke da amarya da wasu ‘yan biki ta faɗa cikin kogi.
Motar ta faɗa cikin a kogin ne a lokacin da take yunƙurin tsallake wata gada da ta karye wadda ke tsakanin ƙauyen Gwalli da garin Gummi a Jihar Zamfara.
Mutanen da abin ya rutsa da su taso ne daga Ƙauyen Fass a Ƙaramar Hukumar Gummi zuwa Jihar Kebbi domin kai amarya wurin mijinta bayan an kammala aure.
Waɗanda suka shaida lamarin sun bayyana cewa direban motar, wanda bai saba da hanyar ba, ya yi ƙoƙarin ƙetare gadar wadda jama’ar ƙauyen suka yi wa cuko da yashi da duwatsu.
A cewar Muhammad Fatihu, motar ta zame daga inda aka cike da duwatsu ta kuma kife a cikin kogi, lamarin da ya jawo nutsewar fasinjojin.
Wani ɗan uwa ga waɗanda abin ya shafa, Ummaru Tela Gwalli, ya bayyana cewa motar ta yi lodi fiye da kima, kuma direban ya firgita a lokacin da ya ji motar tana gogar duwatsun da aka yi amfani da su wajen rufe ramin gadar.
Comments
No comments Yet
Comment