Sport
Dollar
41,3072
-0.13 %Euro
48,5954
0.02 %Gram Gold
4.833,8700
-0.24 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Hakan ya fito ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin-Tofa ya fitar bayan taron majalisar zartarwa ta jiha karo na 31.
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da miƙa wa Majalisar Dokokin jihar wani ƙudiri na haramta auren jinsi da sauran abubuwan da ake ganin ba su da kyau a tsarin addinin Musulunci da na al’ada.
Hakan ya fito ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin-Tofa ya fitar bayan taron majalisar zartarwa ta jiha karo na 31.
Gwamna Yusuf, ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na kare martabar Musulunci da kuma al’adun Jihar Kano. Ya bayyana ƙudurin dokar a matsayin kariya ga mutuncin jihar.
“Babu wani dalili ko yanayi da zai sa mu bar ayyukan da suka saɓa wa addininmu da al’adunmu su yi katutu a Kano, wannan gwamnati wajibi ne ta kare mutuncin al’ummarmu,” in ji shi.
Comments
No comments Yet
Comment