Dollar

41,3070

-0.13 %

Euro

48,5953

0.03 %

Gram Gold

4.834,5700

-0.23 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Wata sanarwa da matatar ta fitar ranar Alhamis ta ce ruɓanya farashin gas din ba zai hana ta fara amfani da tankoki 10,000 domin dakon mai kyauta a fadin Nijeriya ba.

Babu gudu babu ja da baya kan dakon mai kyauta a Nijeriya— Matatar Dangote

Matatar Mai ta Dangote ta ce ba za ta janye shirinta na fara dakon mai kyauta da sabbin tankoki masu amfani da gas din CNG ba duk da ruɓanya farashin gas din da aka yi kwanan nan.

Wata sanarwa da matatar ta fitar ranar Alhamis ta ce ruɓanya farashin gas din ba zai hana ta fara amfani da tankoki 10,000 domin dakon mai kyauta a fadin Nijeriya ba.

Da alama NIPCO, wanda ya fi ƙarfi a harkar CNG a Nijeriya tana wannan ne domin yi wa shirinmu na dakon mai da gas ɗin CNG maƙarƙashiya domin ta gaza aiki,” in ji sanarwar.

Kazalika matatar ta gargaɗi ƙungiyar ƙwadagon ma’aikatan dakon mai ta NUPENG cewa ba za ta lamunci yin zagon ƙasa wa tattalin arziƙi da sunan gwagwarmayar ƙwadago ba. 

“Tun da matatar ta fara aiki, ayyukanmu sun ba da gudunmawa wajen samar wa ƙungiyar kuɗin shiga da ma gudnar da ayyukanta,” in ji matatar.

Duk da cewa muna maraba da tattaunawa mai m’ana, ba za mu lamunci yi wa tattalin arziƙi zagon ƙasa da tilastawa da tursasawa ba domin samun wata biyan buƙata da sunan gwagwarmayar ƙwadago ba,” in ji sanarwar.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#