Dollar

38,8667

0.37 %

Euro

43,3347

-0.38 %

Gram Gold

3.981,6100

-1.29 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Gwarzon tsohon ɗan wasan Barcelona Lionel Messi ya nuna farin cikinsa da jin labarin tsohuwar ƙungiyarsa ta lashe kofin La Liga na 2024-25.

Messi ya taya Barcelona murnar lashe kofin La Liga na bana

Mashahurin ɗan wasan Inter Miami ta Amurka, kuma tsohon gwarzon ɗan wasan Barcelona, Lionel Messi ya miƙa saƙon taya murna ga ƙungiyar, bayan ta tabbata su ne zakarun gasar La Liga ta bana.

A daren Alhamis ne Barcelona ta doke Espanyol da ci 2-0, wanda ya tabbatar mata da lashe kofin La Liga, sakamakon bai wa Real Madrid tazarar da ba za ta iya cim mata ba.

Lashe kofin da ta yi a karo na 28 a kakar bana, shaida ce ta irin tagomashin da Barca ta samu, irin wanda ba ta taɓa samunsa ba tun a zamanin da Messi ke taka musu leda.

Kocin Barca, Hansi Flick ne ya jagoranci ƙungiyar wajen ƙayatar da masoyanta da masu kallon ƙwallo, inda suka zura ƙwallaye 97 a gasar La Liga zuwa yanzu.

Soyayyar Messi ga Barca

Alaƙar Lionel Messi da Barcelona ta kasance mara armashi tun bayan barinsa ƙungiyar a 2021, saboda ya tafi da haushin shugaban ƙungiyar Joan Laporta, wanda ta karya alƙwarin da ya masa na ba shi sabuwar kwantiragi duk da matsalar ƙudin da suke ciki.

A yanzu shekaru huɗu bayan rabuwarsu, masoya Barca na yin tambayoyi kan yadda Messi ke kallon ƙungiyar, saboda ba ya taya su murna idan sun ci wani kofi, saɓanin yadda wasu tsaffin ‘yan wasansu ke yi.

Sai dai a bana, Messi ya sauya tunani inda ya wallafa saƙo a shafinsa na Instagram yana cewa, "Sambarka!"

Tun bayan da a 2023 kwantiraginsa ta ƙare a Paris Saint-Germain, an yi ta raɗe-raɗin cewa Messi zai koma Barcelona.

Amma duk da cewa ƙungiyar da yake a yanzu, Inter Miami tana fama da rashin tagomashi, da wuya Messi ya sauya sheƙa zuwa tsohon gidansa a Catalan, Sifaniya.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#