Dollar

38,8109

0.03 %

Euro

43,6052

0.36 %

Gram Gold

3.962,6600

0.04 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Andy Murray ya daina aiki da Novak Djokovic a matsayin mai horar da shi, bayan kwashe watanni shida ba tare da Djokovic ya yi nasarar cin kofi ba.

Djokovic ya sallami kocinsa Andy Murray gabanin gasar tenis ta French Open

Gwarzon ɗan wasan tenis Novak Djokovic ya raba gari da kocinsa Andy Murray, wanda shi ma tsohon tauraron wasan tenis ne.

Djokovic ya lashe manyan kofunan gasar tenis 24 a rayuwarsa, amma ya kwashe watanni shida na baya-bayan nan ba tare da ya ɗaga wani kofi ba.

Cikin duka watannin, Andy Murray tsohon ɗan tenis ɗan Burtaniya ne ke zaman kocin Djokovic wanda ɗan Serbia ne.

Sai dai ranar Talata nan, gabanin babbar gasar Australian Open ta wannan shekara, wakilan Murray sun bayyana cewa sun raba gari da Djokovic.

A Fabrairun da ya gabata yayin gasar Qatar Open, Djokociv ya faɗi cewa zai ci gaba da aiki tare da Murray ba tare da iyakance lokaci ba.

Sai dai yanzu, haɗin-gwiwarsu ta zo ƙarshe, yayin da yake fatan kawo ƙarshen rashin tagomashinsa a kakar tenis ɗin filin taɓo, a gasar Geneva Open mako mai zuwa.

Sannan akwai gasannin French Open da yake ƙoƙarin lashewa karo na huɗu, da gasar Roland Garros da za a fara ranar 25 ga Mayu.

Sanarwar Murray

Sanarwar Andy Murray ta ce, "Na gode wa Novak saboda damar ban mamaki da muka samu ta aiki tare, da kuma godiya ga tawagarsa saboda ƙoƙarinsu a cikin watanni shida da suka gabata. Ina yi wa Novak fatan alheri a sauran kakar wasa."

A tarihin buga wasa tsakaninsu, Djokovic ya lashe wasanni 25 cikin 36 da suka fafata da Murray.

Djokovic ya kai matakin kusa da ƙarshe a gasar Australian Open a Janairu, amma rauni ya hana shi ƙarasa gasar. Ya kai wasan ƙarshe na Miami Open a watan Maris, amma Jakub Mensik ya doke shi.

Djokovic zai cika shekara 38 kwanaki uku kafin kakar Grand Slam ta biyu a shekarar nan, kuma ya samu mummunan rashin tagomashi tun kayen da ya sha a Miami.

An doke shi a rukunin farkon gasar Masters a Monte Carlo da Madrid, a watan da ya gabata.

An yi tunanin Djokovic zai fara gasar Rome kafin ya je Paris, inda ya lashe zinare na gasar Olympics a bara. Amma ya tsallake gasar Italian Open da ake yi yanzu, ba tare da bayar da dalili ba.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#