Dollar

38,8949

0.36 %

Euro

43,4533

-0.25 %

Gram Gold

3.997,1000

-0.9 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Istanbul na karɓar baƙuncin tattaunawar banarori uku inda Turkiyya ta haɗa Rasha da Ukraine da Amurka waje guda, a wani sabon yunƙuri na kawo ƙarshen yaƙin.

Idanu sun karkata ga Istanbul a yayin da Rasha da Ukraine suka fara tattaunawar zaman lafiya

An fara tattaunawa ta farko kai tsaye a cikin shekaru uku a tsakanin Rasha da Ukraine a ranar Juma’a a Istanbul.

Kiev ta ce suna neman “tsagaita wuta ba tare da sharadi ba”. Morcow kuma na cewa suna son magance “tushen rikicin” tare da dawo wa kan yarjejeniyar 2022 da ba ta yi nasara ba.

An fara ganawar bayan wata gana wa da jami’an Turkiyya da Amurka da Ukraine suka gudanar tare da Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan.

A wani buɗaɗɗen jawabi a wajen taron na Rasha da Ukraine, Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Fidan ya ce: ‘dole mu yi amfani da wannan dama don kusantar hanyar samun zaman lafiya’.

Ya zauna a gaban teburin da ke dauke da tutocin Turkiyya da Rasha da Ukraine - inda wakilan Rasha da Ukraine ke kallon juna, kamar yadda wani bidiyo ya nuna.

Dukkan zaman an yi su ne a Fadar Shugaban Ƙasa ta Dolmabahce, waje mai tarihi da ake yawan yin tarukan diflomasiyya.

Tarukan sun haɗa manyan wakilan bangarorin waje guda.

Wakilin Turkiyya shi ne Ministan Harkokin Wajen kasar Hakan Fidan, wanda ya taka babbar rawa a neman samun zaman lafiyar.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ne ke jagorantar jami’an kasarsa, inda Ministan Tsaron Ukraine Rustem Umerov kuma ya jagoranci tawagar Ukraine. A ɓangaren Rasha, Mai ba wa Shugaban shawara Vladimir Medinsky ne ya jagoranci wakilan ƙasar.

Tawagar Ukraine ta haɗa da Mataimakin ministan Harkokin Waje Sergiy Kyslytsya da Mataimakin Shugaban Tsaro Oleksandr Poklad, da Mataimakin Shugaban Hukumar Leƙen Asiei Oleh Luhovskyi.

Tawagar Rasha ta haɗa da Mataimakin Ministan Harkokin Waje Mikhail Galuzin, da Daraktan Leƙen Asiri Igor Kostyukov, da Mataimakin Ministan Tsaro Aleksandr Fomin, wanda hakan na nufin ƙarfi da muhimmancin tattaunawar.

Kakakin fadar Cremlin, Dmitry Peskov a ranar Juma’a ya ce “dole ne” a yi ganawa tsakanin shugabannin ƙasashen Rasha da Amurka, amma sai an shirya wa hakan tukunna.

Da yake magana ga ‘yan jaridu a Moscow, Peskov ya bayyana cewa alaƙar ƙasashen biyu da batutuwan ƙasa da ƙasa, da rikicin Ukraine ne ya kamata su zama abubuwan da Vladimir Putin da Donald Trump za su tattauna a kai.

“Dole ne a yi wannan ganawa duba da alaƙar ƙasashen biyu, sannan a duba batutuwan kasa da kasa da na yankuna da suke da hannu a rikicin Ukraine,” in ji shi.

Da aka tambaye shi game da tattaunawar zaman lafiya ta ranar Juma’a tsakanin Rasha da Ukraine a Istanbul, Peskov ya ce Putin na samun dukkan bayanai nan da nan. Ya kuma yi tsokaci da cewa shugaban Rasha zai yi wayar tarho ta ƙasa da kasa a ranar Juma’a.

Tattaunawar ta Istanbul na zuwa ne a lokacin da ake sa ran samun ci-gaba, bayan ɗaukar watanni da dakatar da hakan.

Ana kallon ƙoƙarin Turkiyya na haɗa ɓangarorin su tattauna na da muhimmanci, wanda zai samar da zaman lafiya a yankin, da ma duniya baki daya.

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#