Isra'ila ta kashe akalla Falasdinawa 36,171 - kashi 71% daga cikinsu mata ne da yara da jarirai - tare da raunata 81,420 a yakin da ta kwashe kwanaki 237 tana yi a Gaza, in ji jami'an Falasdinawa.

Mayaƙan Houthis sun sha alwashin zafafa kai hare-hare a teku don goyon bayan Gaza

1350 GMT — Mayaƙan Houthis sun sha alwashin zafafa kai hare-hare don goyon bayan Gaza

'Yan Houthi na Yamen sun sha alwashin ci gaba da kai hare-hare cikin azama da karsashi don goyon bayan Falasdinawa a yakin da Isra'ila ke yi a Gaza, kamar yadda shugaban kungiyar da ke samun goyon bayan Iran Abdulmalik al-Houthi ya faɗa a wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin.

Tun a watan Nuwamba ne kungiyar ta kai hare-hare kan jiragen ruwa a yankin Tekun Bahar Maliya, lamarin da ya tilasta wa masu jigilar kayayyaki sauya hanya mai tsawo da tsada a kudancin Afirka.

Daga baya kungiyar ta fadada yawan hare-haren da take kaiwa zuwa Tekun Indiya tare da cewa za ta kuma kai hari kan duk wani jirgin ruwa da ya nufi tashar jiragen ruwa ta Isra'ila a Tekun Bahar Rum.

1038 GMT — Iyalai a Gaza suna fuskantar matsalar lafiyar da ba a taɓa ganin irinta ba — MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa iyalai a Gaza na fuskantar matsalar lafiya mara misaltuwa yayin da Isra'ila ke ci gaba da gwabza yakin ayankin da aka yi wa ƙawanya kusan watanni takwas.

A wani saƙo da aka wallafa a shafin X, Hukumar Ba da Agaji da Ayyuka ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA) ta bayyana gwagwarmayar yau da kullum da mutanen Gazan ke fama da shi, yana mai cewa: “A kowace rana, mutane suna jin rauni da karancin tsafta da yaduwar cututtuka, rashin isasshen abinci da ruwa, da iyakance damar samun magunguna da kiwon lafiya."

"Iyalai a Gaza na fuskantar wani yanayi na gaggawa na lafiya da ba a taba ganin irinsa ba," in ji hukumar, inda ta yi kira da a tsagaita wuta.

0859 GMT — Isra'ila ta umarci UNRWA da ta fice daga hedkwatarta da ke Gabashin Birnin Kudus

Kamfanin dillancin labaran Isra'ila ya rawaito cewa hukumar kula da filaye ta Isra’ila ta umurci hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Falasdinu ta UNRWA da ta fice daga hedikwatarta da ke Gabashin Birnin Kudus da ta mamaye a cikin kwanaki 30.

A cewar shafin yada labarai na Times of Israel, hukumar kula da filaye ta Isra'ila ta ce suna bin UNRWA "kudi har dala miliyan 7,326,711.19 na aiki a filin Isra'ila ba tare da izini ba tsawon shekaru bakwai da suka wuce."

Ana dai kallon matakin da aka dauka kan UNRWA a matsayin na siyasa, yayin da jami'an Isra'ila da suka hada da Firaminista Benjamin Netanyahu suka dade suna neman wargaza UNRWA daga ayyukanta a yankunan Falasdinawa da ta mamaye.

0407 GMT — Shugaban Masar Sisi ya yi kira da a tabbatar ba a 'tursasa wa Falasɗinawa' barin Gaza ba

Shugaban Masar Abdel Fattah el Sisi ya yi kira ga ƙasashen duniya su tabbatar ba a kori Falasɗinawa daga yankin Gaza da Isra'ila ke kai wa hare-hare ba.

"Ina kira ga ƙasashen duniya su yi gaggawar kai kayan agaji na tsawon lokaci zuwa Zirin Gaza sannan su tabbatar da kawo ƙarshen ƙawanyar da ake yi wa yankin," in ji Sisi a taron da shugabannin ƙasashen Larabawa da China suka halarta a Beijing.

Kazalika ya yi kira ga ƙasashen duniya su "dakatar da duk wani yunƙuri na tursasa wa Falasɗinawa barin ƙasarsu"

0330 GMT — Shugaban China Xi Jinping ya yi kira da a gudanar da taron zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falasdinu

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kira taron zaman lafiya game da yakin da Isra'ila ke yi kan Gaza da ta yi wa kawanya a lokacin da yake jawabi ga shugabannin kasashen Larabawa da jami'an diflomasiyya a wani dandalin tattaunawa a birnin Beijing.

A wannan makon ne kasar Sin za ta karbi bakuncin shugaban kasar Masar Abdel Fattah el-Sisi da wasu shugabannin kasashen Larabawa da dama, domin halartar wani taron tattaunawa kan yakin Gaza.

Da yake jawabi ga tawagogin a safiyar ranar Alhamis, Xi ya ce, kasar Sin tana goyon bayan wani babban taro na zaman lafiya domin warware rikici. Xi ya ce "Gabas ta Tsakiya yanki ne da ake yi wa kyakkyawan fata na samun ci gaba, amma har yanzu yaƙi yana ci gaba da ruruwa a can."

Ya kara da cewa "Bai kamata a ci gaba da yaki ba har abada. Bai kamata a ce an kasa yin adalco ba har abada."

Xi ya kuma ce, China tana goyon bayan kasancewar Falasdinu cikakkiyar mamba a MDD, kuma tana goyon bayan babban taron zaman lafiya na kasa da kasa mai tushe, mai iko da inganci.

China, wadda ke da kyakkyawar alaka da Isra'ila, ta sha gabatar da shawarwarin samar da kasashe biyu na warware rikicin Isra'ila da Falasdinu tsawon shekaru da dama.

Shugaba Xi ya ce bai kamata a ci gaba da yaki ba har abada. / Hoto: AFP

2130 GMT — An kori ma'aikaciyar jinyar da aka bai wa lambar yabo kan tausayi bayan yin magana game da kisan kare dangi a Gaza

Wani asibitin birnin New York ya kori wata ma’aikaciyar jinya bayan da ta yi nuni da yakin da Isra’ila ke yi a Gaza a matsayin kisan kiyashi a lokacin da take jawabin karbar lambar yabo.

Ma’aikaciyar jinya da haihuwa Hesen Jabr, ‘Ba'amurkiya kuma Bafalasdiniya ce, wadda hukumar lafiya ta NYU Langone ta karrama ta saboda tausayin da take nunawa wajen kula da iyaye mata da suka rasa jariransu, take kuma alaƙanta aikinta da wahalar da iyaye mata ke sha a Gaza.

Jabr ta ce, "Na ji zafi ganin yadda matan kasata ke tafka asara da ba za a iya misaltawa ba, a lokacin da ake yin kisan kare dangi a Gaza," in ji Jabr, a cikin wani bidiyo na jawabin da ta yi ranar 7 ga Mayu da ta wallafa a shafukan sada zumunta. "Wannan lambar yabo mai karfi ce a gare ni saboda waɗannan dalilai."

Jabr ta rubuta a shafinta na Instagram cewa ta isa wurin aiki a ranar 22 ga Mayu don komawarta ta farko bayan samun lambar yabo lokacin da aka gayyace ta wata ganawa da shugaban asibitin da mataimakin shugaban ma'aikatan jinya "don tattauna yadda na sanya wasu cikin haɗari" da yadda "na lalata bikin karramawar" da "ɓata wa mutane rai" saboda a jawabina na nuna 'yar girmamawa ga iyaye mata 'yan kasata da ke cikin bakin ciki a kasata."

Ta rubuta cewa bayan da ta yi aiki na dan lokaci sai aka sake kiran ta zuwa wani ofishi inda aka karanta takardar dakatar da ita sannan aka fitar da ita daga asibitin.

#