Dollar

40,3777

0.14 %

Euro

46,9177

0.07 %

Gram Gold

4.325,4300

-0.16 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Shugaba Ahmad al Sharaa ya jinjina wa Amurka da Turkiyya da ƙasashen Larabawa dangane da rawar da suka taka wurin shiga tsakani da kuma ceto yankin daga makoma maras tabbas.

Masu shiga tsakani sun wargaza shirin Isra'ila na hargitsa Gabas ta Tsakiya: Syria

Shugaban Syria, Ahmed al Sharaa, a ranar Alhamis ya bayyana cewa shirye-shiryen Isra'ila na kawo rashin zaman lafiya a yankin ya ci tura sakamakon ayyukan masu shiga tsakani daga waje da kuma ƙoƙarin gwamnatin Syria.

A cikin wani jawabi ta talabijin, Al Sharaa ya ce: "Ba mu daga cikin waɗanda ke tsoron yaki. Mun shafe rayuwarmu muna fuskantar ƙalubale da kare mutanenmu, amma mun fifita muradun 'yan Syria fiye da shiga cikin rikici da lalata wurare."

Al Sharaa ya kuma bayyana cewa duk da hare-haren Isra'ila da ta kai kan fararen hula da cibiyoyin gwamnati, "kokarin gwamnati na dawo da zaman lafiya da kuma korar ƙungiyoyin da ba su bin doka ya yi nasara."

Wannan ba zai yiwu ba "ba tare da shiga tsakani mai tasiri daga Amurka, ƙasashen Larabawa, da Turkiyya ba, wanda ya ceci yankin daga makoma wadda ba ta da tabbaci," in ji shi.

A ranar Laraba ne sojojin Isra'ila suka kai hare-hare ta sama a birnin Damascus da kuma yankunan Sweida da Daraa bisa hujjar kare al'ummar Druze.

Ma'aikatar Cikin Gida ta bayyana cewa hare-haren sun kashe fiye da mutane 30 tare da jikkata kusan 100.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#