Sport
Dollar
40,2266
0.13 %Euro
46,9254
-0.35 %Gram Gold
4.331,1500
-0.09 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Ko da an cim ma tsagaita wuta, Isra’ila ta ce tana da shirin ci gaba da ajiye sojojinta a wasu yankunan Falasdinawa.
Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya ce yana fatan nan da wani dan lokaci za a cim ma yarjejeniya a Gaza tsakanin Isra’ila da kungiyar gwagwarmaya ta Falasdinawa ta Hamas.
“Gaza - muna magana, kuma muna sa ran za mu samu tabbacin hakan a mako mai zuwa,” in ji Trump ya fada wa manema labarai a Sansanin Hadin Gwiwa na Andrews da ke Maryland a ranar Lahadi.
A baya Trump ya bayyana cewa Isra’ila ta amince da da sharuddan tsagaita wuta na kwanaki 60 a Gaza, inda Qatar da masar suka mika wa Hamas kudirin yarjejeniyar.
Hamas ta bayar da amsar amincewa inda ta ce ta shirya shiga sulhun da tattaunawar don tabbatar da tsagaita wuta da musayar fusunoni.
‘Sansanin tattara jama’a’
Duk da Isra’ila ta ce ba za a amince da sauye-sauyen da Hamas ta nema a yi a cikin kudirin yarjejeniyar ba, wakilanta za su tafi Doha don tattaunawa.
Tattaunawar Doha ta mayar da hankali kan tsagaita wuta na kwanaki 60, rakin Isra’ilawa 10 da ke da rai da 18 da suka mutu da kuma tattaunawa kan yarjejeniyar dindindin.
A yayin da aka samu rahotannin warwre batutuwa da dama, batun da ake ta ja in ja shi ne nacewar da Isra’ila ta yi na ci gaba da dabbaka iko a yankunan zaman lafiya na Gaza.
Ko da an cim-ma tsagaita wuta, Isra’ila ta bayyana shirinta na ci gaba da kula da Rafah tare a ka kafa “sansanin tattara jama’a” a wani bangare na manufarta ta korar Falasdinawa zuwa wasu kasashen.
Comments
No comments Yet
Comment