Dollar

40,1901

0.22 %

Euro

47,1146

0.08 %

Gram Gold

4.336,9600

1.24 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

An haifi Zuq a shekarar 2008 a cikin gidan yarin Hasharon na Isra'ila bayan an kama mahaifiyarsa Fatima al-Zuq a shekarar 2007 tana ɗauke da cikinsa.

Youssef al-Zuq : An haife shi a kurkukun Isra’ila, sannan Isra’ilar ta kashe shi bayan shekara 17

Wani yaro ɗan shekara 17 ɗan asalin Falasɗinu, wanda aka taɓa saninsa a matsayin mafi ƙarancin shekaru a duniya da aka sake shi daga kurkuku, ya rasa ransa a wani hari ta sama da Isra'ila ta kai a tsakiyar Gaza, in ji Ofishin Yaɗa Labaran Fursunonin Falasɗinu.

Youssef al-Zuq ya rasu bayan wani jirgin sama mara matuƙi na Isra'ila ya kai hari kan gidansu a kan titin Al-Thawra da ke birnin Gaza da sanyin safiyar Asabar, a cewar wata sanarwa daga ofishin.

An haifi Zuq a shekarar 2008 a cikin gidan yarin Hasharon na Isra'ila bayan an kama mahaifiyarsa Fatima al-Zuq a shekarar 2007 tana ɗauke da cikinsa.

Fatima tana kan hanyarta ta barin Gaza don neman magani a lokacin da sojojin Isra'ila suka kama ta. Daga baya ta gano tana da ciki a lokacin da take tsare, kuma ta haifi Youssef a cikin kurkuku.

Ta raini Youssef na kusan shekaru biyu a cikin mawuyacin yanayi a kurkukun, inda ta yi fama da rashin kula ta fannin lafiya da rashin abinci mai gina jiki da kuma rashin kulawa ta musamman ga jaririnta, kamar yadda rahotannin ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan’adam na baya suka bayyana.

An saki Youssef da mahaifiyarsa a shekarar 2009 a yayin wata yarjejeniya inda Isra'ila ta saki matan Falasɗinu 19 a madadin wani bidiyo da ke tabbatar cewa wani sojan Isra'ila Gilad Shalit yana raye a hannun Hamas.

Daga baya an saki Shalit a cikin wata babbar yarjejeniya ta musayar fursunoni a shekarar 2011.

Harin da aka kai a ranar Asabar wanda ya kashe Youssef al-Zuq ya kasance ɗaya daga cikin hare-hare ta sama masu tsanani da Isra'ila ta kai a Gaza.

Aƙalla Falasɗinawa 100, ciki har da mutane 27 da ke neman agaji, suka rasa rayukansu a hare-hare ta sama da Isra'ila ta kai a wurare daban-daban na Gaza a ranar Asabar, a cewar majiyoyin lafiya.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#