Sport
Dollar
39,1011
0.04 %Euro
44,4609
0.52 %Gram Gold
4.202,2600
1.92 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Hamas ta ce dakarunta na Qassam Brigades sun yi wa sojojin na Isra'ila kwanton-ɓauna a kudancin Gaza sannan kuma suka yi amfani da bam domin tarwatsa wani gida da sojojin na Isra'ila suka ɓoye a Khan Younis
Ƙungiyar gwagwarmayar Falasɗinawa ta Hamas a ranar Lahadi ta sanar da cewa ta kashe sojojin Isra’ila da dama tare da jikkata wasu a yayin wani kwanton-ɓauna da ta yi musu a kudancin Gaza.
Sashen dakaru masu ɗauke da makamai na Hamas wato Qassam Brigades sun ce mayaƙansu sun tarwatsa wani gida da bam a ranar Talata, wanda a cewarsu gida ne da sojojin na Isra’ila suka ɓoye a gabashin birnin al-Qarara da ke Khan Younis.
Ƙungiyar Hamas ta ce sojoji da dama ne suka mutu a wurin wasu kuma suka jikkata.
Hamas ɗin ta ce dakarunta sun tarwatsa wata ƙofar shiga ginin na ƙarƙashin ƙasa a daidai lokacin da sojojin na Isra’ila suka isa wurin, inda aka ga jirgi mai saukar ungulu na Isra’ila na ɗaukar waɗanda suka jikkata.
Sojojin na Isra’ila ba su ce komai ba dangane da ikirarin na Hamas.
Duk da kiraye-kirayen da ake yi na tsagaita wuta, Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare ba ƙaƙƙautawa a Gaza inda sojojin na Isra’ila suka kashe fiye da Falasɗinawa 53,900, waɗanda akasarinsu mata ne da yara.
A watan Nuwamban da ya gabata ne Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya ta bayar da sammacin kama Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da tsohon ministan tsaronsa Yoav Gallant bisa laifukan yaki da cin zarafin bil'adama a Gaza.
Haka kuma Isra’ila na fuskantar shari’o’i a gaban Kotun Duniya kan kisan kiyashin da take aikatawa a Gaza.
Comments
No comments Yet
Comment