Sport
Dollar
38,9193
0.11 %Euro
44,0186
-0.17 %Gram Gold
4.125,0300
-0.43 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%‘Tabbas muna goyon bayan mafitar samar da ƙasashe biyu,’ in ji Ministan Harkokin Wajen Angola, Tete Antonio.
Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU) “ba za ta iya farinciki ba a lokacin da ake ƙoƙarin kora Falasɗinawa zuwa Afirka,” in ji Ministan Harkokin Wajen Angola Tete Antonio.
“Tabbas muna goyon bayan mafita ta samar da ƙasashe biyu, ƙasashe biyu a gefen juna da kuma ƙudirin MDD a yanzu,” kamar yadda Antonio ya sanar da wani taron manema labarai da Babbar Jami’ar Ƙungiyar Tarayyar Turai Kaja Kallas ranar Laraba, bayan zaman ministocin EU da AU a Brussels.
“Muna kusa da yankin, kuma ba ma nuna halin rashin kulawa ga wahalar waɗannan mutanen,” in ji shi.
Wannan na zuwa ne yayin da Amurka ke ƙoƙarin korar sama da Falasɗinawa miliyan ɗaya daga Gaza, inda hare-haren Isra’ila suka kashe sama da mutum 50,000 tun watan Oktobar shekarar 2023.
Antonio ya ce halin AU“ na nuna kula zai ci gaba da kasancewa a duk inda ake rikici da kuma game da Falasɗinawa.”
Ya ce baƙo ɗaya tilo da aka yi wa gayyata ta din-din-din zuwa taron AU shi ne shugaban Falasɗinawa, yana mai ƙarawa da cewa halin da Falasɗinawa ke ciki batu ne da ƙungiyar ta damu da shi ne sosai.
‘Yaƙin farfaganda’
Kallas, a nata ɓangaren, ta ce yanayin da ake ciki a yankin Sahel na Afirka “abin damuwa ne sosai” ga ƙungiyar EU, kuma ƙungiyar za ta tattauna game da “wata sabuwar dabarar Sahel.”
“Na gudanar da tattaunawa da ƙasashe da yawa a yau, kuma ina neman ƙasashen Afirka su ƙara shawarwarinsu a kai,” in ji ta.
Yayin da take bayyana goyon bayanta ga AU da matakan da take ɗaukawa na shiga tsakani a yankin, ta jaddada cewa: “Dukkan waɗannan matakan har ma cikin Afirka dole su kasance ‘yan Afirka ne ke jagorantar su kuma su kasance mallakin ‘yan Afirka, ko ma idan akwai ɓauƙatar shiga tsakani.”
Kallas ta kuma bayyana cewa akwai “yaƙin farfaganda” a ko ina, “kuma watsa labaran ƙarya ɗaya ne daga cikin kayayyakin aikin da Rasha ke amfani da su, musamman a Afirka.”
“Dole mu yaƙi watsa labaran ƙarya da kuma zagon ƙasa daga ƙetare a ko wane lokaci,” in ji ta.
Comments
No comments Yet
Comment