Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda ya shiga kwana na 327, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 40,476— galibinsu mata da yara — tare da jikkata fiye da mutum 93,647, sannan an yi amanna cewa ɓaraguzan gine-gine sun danne fiye da mutum 10,000.

NEWSTIMETR
NEWSTIMETR
Kai-tsaye: Umarnin da Isra'ila ta bayar na ficewa a Gaɓar Yamma ya saɓa dokokin duniya — Hamas

Laraba, 28 ga watan Agusta 2024

Ƙungiyar gwagwarmaya ta Falasɗinawa Hamas ta yi tir da kiran da Isra’ila ta yi na a ba da umarnin ficewa a Gaɓar Yamma da aka mamaye irin yadda ake yi wa Falasɗinawa a Gaza, abin da ta ce “ya saɓa wa dokokin duniya.”

Ministan Harkokin Ƙasashen Waje na Isra’ila Katz ya yi kira da a a yi wa Falasdinawa a arewacin Gaɓar Yamma, kamar yadda ake yi a Gaza, har da ficewa daga gidaje.

“(Wannan) kira ne na zalunci don faɗaɗa irin ɓarnar da ake yi, da kisan kiyashi, da ƙoƙarin ƙarar da Falasɗinawa,” kamar yadda Shugaban Hamas Izzat al Rishaq ya faɗa a cikin wata sanarwa.

“Kiran ya nuna irin yadda Isra’ila ke matuƙar saɓa dokokin duniya, kuma abin na nuna irin yadda shugabannin gwamnatin ke cin karensu ba babbaka, waɗanda suke kauce wa duk wani hukunci kan yadda suke cin zarafin ɗan adam.”

Shugaban Hamas ya yi kira ga ƙasashen duniya da Majalisar Ɗinkin Duniya su yi “gaggawar janye duk wata kariya da gwamnatin Amurka ke samar wa masu aikata laifukan yaƙi na Isra’ila.

0726 GMT — Ministan harkokin wajen Isra'ila ya yi barazanar tursasawa a kwashe Falasɗinawa daga yankunan arewa da Gaɓar Yammacin Kogin Jordan a yayin da suke ci gaba da kutsawa yankin.

Tun da farko rundunar sojin Isra'ila ta ƙaddamar da samame a yankunan arewa da Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, da suka haɗa da biranen Jenin, Tulkarem da Tubas, inda kawo yanzu suka kashe Falasɗinawa 11.

A sanarwar da ya wallafa a shafin X, Israel Katz ya ce sojojin ƙasarsu suna aiki a Jenin da Tulkarem domin daƙile abin da ya bayyana "ayyukan 'yan ta'adda a kan Isra'ila a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan."

Ya ƙara da cewa samamen da sojoji suka kai ya haɗa da "kwashe Falasɗinawa mazauna yankunan arewa da Gaɓar Yammacin Kogin Jordan na ɗan wani lokaci" kamar yadda suka yi a Gaza.

0418 GMT —Isra'ila ta kashe Falasɗinawa da dama a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan

Isra'ila ta kashe Falasɗinawa aƙalla goma a hare-hare ta sama da samame da ta kai a wasu garuruwa da ke arewa da Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, a cewar mai magana da yawun ƙungiyar bayar da agaji ta Red Crescent.

Jiragen yaƙin Isra'ila sun kashe Falasɗinawa biyu a birnin Jenin, da kuma mutum huɗu a wani ƙauye da ke maƙotaka da birnin, da mutum huɗu a wani sansanin 'yan gudun hijira da ke kusa da garin Tubas, in ji Ahmed Jibril, jami'in ƙungiyar bayar da agajin.

An kashe Falasɗinawa biyu a birnin Jenin, da kuma mutum huɗu a wani ƙauye da ke maƙotaka da birnin, da mutum huɗu a wani sansanin 'yan gudun hijira da ke kusa da garin Tubas./Hoto: AA

0123 GMT — Shugaban Falasɗinawa da Yarima Mai Jiran Gadon Sarautar Saudiyya sun tattauna kan yaƙin Isra'ila a Gaza

Shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas da Yarima Mai Jiran Gadon Sarautar Saudiyya Mohammed bin Salman sun gana a Riyadh inda suka tattaunawa kan yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza da aka mamaye.

Yayin ganawar tasu, Abbas da Bin Salman sun yi waiwaye kan halin da Falasɗinawa suka faɗa a ciki da kuma yanayin da yankin Gabas ta Tsakiya yake ciki. Kazalika sun tattauna kan yunƙurin Falasɗinawa da ƙasashen Larabawa na ganin Isra'ila ta daina kai hare-hare kan Falasɗinawan Gaza da Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, ciki har da Birnin Ƙudus.

Shugaba Abbas ya yi gargaɗi game da hatsarin kalaman da Isra'ila ta yi game da yiwuwar mamaye wurare masu tsarki na Musulmai da Kiristoci, musamman kalamin da Ministan Tsaron Ƙasar mai tsattsauran ra'ayi Itamar Ben-Gvir ya yi cewa za su gina wurin bautar Yahudawa a cikin Masallacin Ƙudus, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Falasɗinu (WAFA) ya rawaito.

#