Mummunan yaƙin Isra’ila a Gaza yanzu ya shiga rana ta 248, ya kashe aƙalla Falasɗinawa 73,084 — kaso 71 mata da yara da jarirai — ya kuma jikkata mutane 84,494.
0030 GMT — Firaministan Benjamin Netanyahu ya yi kakkasar suka ga Ministan Majalisar yaƙi Benny Gantz saboda murabus daga gwamnatin gaggawa.
Gantz ya sanar da murabus ɗinsa ne tun da farko a ranar Lahadi, yana ambato muhimman bambance-bambance a yadda ake tafi da al’amura, yana da’awar cewa Netanyahu “ya hana mu cim ma ainihin nasara” a yaƙin da muke a Gaza.
Shi ma wani mai sa ido a majalisar ta yaƙi Gadi Eisenkot, wani tsohon shugaban ma’aikata a rundunar sojan Isra’ila, ya sanar da murabus ɗinsa.
Netanyahu ya faɗa a wani saƙo da ya wallafa a X cewa "Isra'ila na yaƙin ƙoƙarin wanzuwa daga ɓangarori da dama. Bany, yanzu ba lokaci ne na watsi da yaƙin ba, lokaci ne na haɗa ƙarfi waje guda."
“Ƙofata za ta ci gaba da kasancewa a buɗe ga duk ɗan jam’iyyar Yahuduwa dake son ɗaukar wannan nauyi ya kuma taimaka mu yi nasara a kan abokan gabarmu da kuma tabbatar da tsaron 'yan kasarmu,” kamar yadda ya bayyana.
Ministan Tsaron Ƙasar mai tsattsauran ra’ayi Itamar Ben-Gvir ya nemi shiga Majalisar Yaƙin bayan Murabus ɗin Gantz. “Dangane da murabus ɗin Gantz, na miƙa buƙata ga Firaminista ina roƙonsa in shiga Majalisar ta Yaƙi.
Lokaci ne na ɗaukar mataki na jarumta, na samar da tsaro na gaskiya, sannan a samar da tsaro ga Kudu da Arewa da gaɓa ɗayan Isra’ila,” kamar yadda Ben-Gvir ya faɗa a saƙon da ya wallafa a X.
