Tsawon kwanaki 105, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 24,700 da raunata mutum 61,830.

KAI-TSAYE: Jarirai kusan 20,000 aka haifa a Gaza tun fara yakin Isra'ila a yankin

1230 GMT — Jarirai kusan 20,000 aka haifa a Gaza tun fara yakin isra'ila a yankin

Jarirai kusan 20,000 aka haifa ana cikin yakin da Isra'ila ke yi a Gaza, yayin da yara 135,000 ke fuskantar "mummunan haɗarin kamuwa da tamowa" a Gaza, a cewar UNICEF a ranar Juma'a.

Mai magana da yawun UNICEF Tess Ingram ya kuma ce adadin ya yi daidai da jariri daya da ake haifa kusan kowane minti 10 tun daga ranar 7 ga Oktoba, lokacin da rikicin ya fara.

Ya shaida wa manema labarai a Geneva cewa: "Halin da mata masu juna biyu da jarirai ke ciki a Zirin Gaza ya wuce gona da iri, kuma yana buƙatar gabatar da ayyuka na gaggawa."

"Halin ha'u'la'in da yara da mata ke ciki har yake sanadin mutuwarsu ya sake ta'azzara, sakamakon rushewar da tsarin kiwon lafiyar ke ciki," Ingram ya jaddada, yana mai cewa uwaye na fuskantar wasu irin ƙalubale masu ta da hankali ta wajen kula da lafiyarsu, da abincin da za su ci musamman a lokacin ciki da goyo.

1108 GMT — Yawan mutanen da aka kashe a hare-haren Isra'ila a Gaza ya ka

The health ministry in Gaza has said Israel's bombardment has killed 24,762 people in the besieged Palestinian territory.

Ma'aikatar Lafiya a Gaza ta ce harin bam da Isra'ila ta kai ya kashe mutum 24,762 a yankin Falasdinawa da aka yi wa kawanya.

Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta ce adadin ya hada da mutum 142 da suka mutu a cikin sa'o'i 24 da suka gabata, yayin da mutum 62,108 suka samu raunuka tun bayan da Isra'ila ta kaddamar da hare-hare ba kakkautawa a ranar 7 ga watan Oktoba bayan harin Hamas.

#