Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda yau ya shiga kwana na 296, ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla 39,258 —  galibinsu mata da yara –– tare da jikkata mutum kimanin 90,589, sannan an yi amanna sama da mutum 10,000 na danne a cikin ɓaraguzai.

Kai-tsaye: Isra'ila ta matsa ƙaimi wurin kai samame a sansanonin 'yan gudun hijira na Gaɓar Yammacin Kogin Jordan

Lahadi, 28 ga watan Yuli, 2024

0038 GMT — Sojojin Isra'ila sun kai samame a sansanin 'yan gudun hijira na Balata da ke gabashin Nablus a arewacin Gaɓar Yamma da Kogin Jordan ranar Asabar da maraice a karo na huɗu cikin awanni 24.

Kamfanin dillancin labarai na Falasɗinu, Wafa, ya ruwaito cewa dakarun Isra'ila sun kutsa cikin sansanin inda suka buɗe wuta, tare da yin amfani da gwanayen harbi na ɓoye da kuma manyan motocin rusa gine-gine.

Masu fafutuka a shafukan sada zumunta sun yi ta wallafa bidiyoyin da ke nuna ƙarin dakarun Isra'ila suna shiga cikin sansanin tare da jin ƙarar harbe-harbe, inda suka yi iƙirarin cewa ana yin ba-ta-kashi ne tsakanin ƙungiyoyin Falasɗinawa da sojojin na Isra'ila.

Sojojin sun fice daga sansanin da tsakar dare bayan sun shafe awanni suka cin zarafin jama'a tare da kashe aƙalla mutum biyu da jikkata gommai, a cewar ganau da kuma hukumomin kiwon lafiya na Falasɗinu.

A yayin da Isra'ila ke yaki a Gaza, a gefe guda kuma tana ci gaba da kai samame a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, lamarin da ya kai ga mutuwar mutum 592 tare da jikkata mutum 5,400, a cewar alƙaluma daga hukumomin Falasɗinu.

An daɗe ana tayar da jijiyoyin wuya a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan da Gabashin Birnin Ƙudus da aka mamaye, a yayin da Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare a Gaza waɗanda suka yi sanadin mutuwar Falasɗinawa kusan 39,300 tun daga ranar 7 ga watan Oktoba.

#