Yakin da Isra'ila ke yi a Gaza ya shiga kwanaki 317 yanzu, ya kashe fiye da Falasdinawa 40,074 akasari mata da ƙananan yara da jikkata mutum fiye da 92,537, an ƙiyasta fiye da 10,000 na binne a ƙarƙashin baraguzan gine-ginen da aka kai musu hari.
Lahadi, 18 ga August, 2024
2100 GMT — Wani harin sama da Isra'ila ta kai yankin Gaza da aka mamaye ya kashe aƙalla mutane 18, dukkansu daga gida ɗaya, sa'o'i bayan masu shiga tsakani sun bayyana kyakkyawan fatan cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta.
Harin na jirgin sama ya afka wa wani gida da wani wajen ajiye kaya inda mutanen da suka rasa gidajensu suke samun matsugunni, a wajen shiga garin Zawaida, kamar yadda Asibitin Shahidai na Al-Aqsa a Deir al-Balah inda aka kai mutanen ya bayyana.
2255 GMT — Isra'ila ta yi da'awar an kashe mata manyan sojoji biyu a Gaza
Wani bam da ƙungiyoyin gwagwarmaya na Falasɗinawa suka ɗana a gefen hanya ya kashe manyan Sojojin Isra'ila biyu a tsakiyar Gaza, a cewar sojoji.
Ɗaya daga cikinsu, jami'in mai kula da kayayyaki Manjo Yotam Itzhak Peled mai shekara 34 na "BataliyarJerusalem Brigade ta 8119 ... bam ɗin da Hamas ta dasa a gefen hanya ne ya kashe shi," a cewar rundunar sojan a cikin wata sanarwa.
A cikin wata sanarwar daban kuma, ta ce jami'i na biyu shi ne Sa Manja Mordechai Yosef Ben Shoam.
Shi ma mai shekaru 34, "direban babbar mota a BataliyarJerusalem Brigade ta 8119 ... yana cikin tawagar da suke kan hanyar kai wa sojojin Isra'ila kayayyaki a yankin Zeitoun na birnin Gaza," kamar yadda sanarwar ta bayyana.