Wannan shafin yana kawo muku sabbin bayanai a ranar Asabar 23 ga watan Disamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba.

KAI-TSAYE: Isra'ila ta kashe mutum 76 'yan gida daya a Gaza

1314 GMT — Isra'ila ta kashe mutum 76 'yan gida daya a Gaza

Wani hari ta sama da Isra’ila ta kai ya yi sanadin mutuwar mutum 76 wadanda suka fito dangi guda, kamar yadda jami’an da ke aikin ceto suka tabbatar.

Wannan na zuwa ne kwana guda bayan shugaban Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadi kan cewa babu wani wuri mai aminci da mutum zai iya tsira a Gaza.

Harin wanda aka kai a gidan iyalan Mughrabi, ya yi sanadin mutuwar masu gidan 16, sai kuma mata da yara da dama.

Daga cikin wadanda suka rasu har da Issam al Mughrabi, wani babban ma’aikacin Majalisar Dinkin Duniya, inda aka kashe shi da matarsa da ‘ya’yansa biyar.

#