Tsawon kwanaki 103, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 24,285 da raunata mutum 61,154.
0745 GMT — Isra'ila ta kashe Falasdinawa 13 a Khan Younis
Akalla Falasdinawa 13 Isra’ila ta kashe a hare-haren da ta kai Khan Younis da ke kudancin Gaza, kamar yadda wani rahoto ya bayyana.
Bayan haka akwai kuma wasu gomman Falasdinawan da suka samu rauni a hare-hare ta sama da kasa, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Falasdinu WAFA ya tabbatar.
Haka kuma ya ce jiragen yakin na Isra’ila sun kai hari kan gidajen Falasdinawa a yammacin Khan Younis.
