A rana ta 328 da Isra’ila ta fara yaki a Gaza, ta kashe a kalla Falasdinawa 40,602 – mafi yawan su mata da yara – tare da jikkata sama da 93,855, inda hasashe ya bayyana sama da mutum 10,000 na karkashin buraguzan gidajen da aka yi wa ruwan bam.

Kai-tsaye: Goyon bayan Amurka ga Isra’ila ne ke hana tsagaita wuta a Gaza — Hamas

Alhamis, 29 ga watan Agusta, 2024

1534 GMT — Jami'in Hamas Sami Abu Zuhri ya ce Amurka na goyon bayan matakin Isra'ila na kin amince wa da tsagaita wuta, wanda hakan ke bayyana rashin niyyar Amurka na dakatar da Tel Aviv daga kai harehare kan Gaza.

Zuhri ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa Amurka ba ta da niyyar matsa lamba ga isra'ila kan ta yarda ta tsagaita wuta a Gaza, yana mai lura da cewar Isra'ila na ci gaba da saka sabbin sharudda saboda goyon bayan Amurka.

Ya bayyana cewa jinkirin da ake samu na tsagaita wuta da musayar fursunoni na zuwa ne saboda wannan yanayi.

Ya kara da cewa "Hamas ta amince da masu shiga tsakani na Masar. Qatar da Amurka suka gabatar a ranar 2 ga Yuli, amma Isra'ila ta saka sabbin sharudda, duk da wannan kudiri na cikin abubuwan da Shugaba Biden ya fada a jawabinsa ga Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya."

Game da matsayar Hamas, Zuhri ya ce "Mun sake jaddada niyyarmu ga kudirin na 2 ga Yuli kuma muna son shirin da zai aiwatar da wannan yarjejeniya."

0849 GMT — Isra'ila ta kashe wani kwamandan ƙungiyar Islamic Jihad a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan

Ƙungiyar Falasɗinawa ta Islamic Jihad ta sanar da mutuwar kwamandanta a sansanin 'yan gudun hijira na Nur Shams da ke yankin Tulkarem na Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye.

Da farko, rundunar sojin Isra'ila ta sanar da kashe mayaƙa 'yan gwagwarmaya biyar, ciki ar da Muhammad Jabber, wanda aka fi sani da Abu Shujaa.

"Abu Shujaa, kwamandan Rundunar Tulkarem Brigade da ke ƙarƙashin Rundunar Al-Quds," wato ɓangaren gwagwarmaya na Islamic Jihad, da ke da ƙarfi a sansanonin 'yan gudun hijira a arewacin Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, "ya mutu ne tare da 'yan'uwa da dama na rundunar bayan sun gwabza faɗa da sojojin Isra'ila masu mamaya", a cewar sanarwar da ƙungiyar ta fitar.

2000 GMT —'Yan jam'iyyun adawar Isra'ila sun amince su kawar da Netanyahu a yayin da yake ci gaba da kai hare-hare a Gaza

Shugaban 'yan Dimokuraɗiyya Yair Golan ya yi kira ga shugabannin jam'iyyun adawa a Isra'ila su gudanar da taron gaggawa domin kawar da gwamnatin Firaminista Benjamin Netanyahu.

Wani saƙon murya da Golan ya wallafa a shafinsa na X ya ce, "A yau, na tuntuɓi dukkan abokaina a jam'iyyun adawa inda na gaya musu saƙona ƙarara cewa ya kamata mu kama hanya iri ɗaya."

Ya ƙara da cewa, "Isra'ila tana cikin mawuyacin hali kuma tana durƙushewa a fannin siyasa da fannin tattalin arziki da mu'amala da kundin tsarin mulki.

"Komai yana wargajewa a idanunmu. Dole mu yi aiki tare kuma cikin tsanaki tare da jajircewa."

Golan ya wallafa saƙon da ya tura wa shugabannin jam'iyyun adawa, da ke cewa: "Muna tsaka da yaƙi, inda aka kwashe kwana 328 ana garkuwa da mutanenmu, kana an raba dubban mutane da gidajensu, sannan tattalin arzikinmu yana durƙushewa, kuma sojojinmu sun kwashe tsawon lokaci suna yaƙi ba tare da samu mafita ba.

"Rashin amincewa da gwamnati da kuma matakan da take yin gaban kanta wajen ɗaukarsu bisa muradunta na siyasa su suka tilasta mana yin wannan yunƙuri."

Da yake yin martani ga saƙon Golan, shugaban jam'iyyun adawa a Isra'ila Yair Lapid ya wallafa saƙo a shafinsa na X da ke cewa, "Za mu ci gaba da yin aiki da dukkan 'yan adawa, a fili da kuma a bayan-fage, har sai mun kawar da wannan gwamnati da ta jefa ƙasarmu cikin bala'i."

Shugaban jam'iyyun adawa a Isra'ila Yair Lapid ya wallafa saƙo a shafinsa na X da ke cewa, "Za mu ci gaba da yin aiki da dukkan 'yan adawa, a fili da kuma a bayan-fage, har sai mun kawar da wannan gwamnati da ta jefa ƙasarmu cikin bala'i." / Hoto: Reuters
#