Isra'ila ta kwashe kwana 278 tana luguden wuta a Gaza inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 38,243 — galibinsu mata da yara –– sannan ta jikkata fiye da mutum 88,033, kana sama da mutum 10,000 na binne a ɓaraguzai.

Kai-tsaye: Amurka ta ce Iran na yunƙurin tunzura jama'a yayin da Isra'ila ke ci gaba da ta'annati a Gaza

2239 GMT — Fadar White House ta zargi Iran da amfani da abin da ke faruwa a Amurka saboda rikicin Gaza don shisshigi cikin lamuran Amurka, tana mai bayyana lamarin a matsayin abin da ba za a amince da shi ba, bayan wani gargaɗi da wani babban jami'in tattara bayanan sirri na Amurka ya yi cewa Iran na son rura wutar yanayin da ake ciki a Amurka.

Gargaɗin, wanda Daraktan Hukumar Leƙen Asirin ƙasar Avril Haines ya yi ya ce wasu mutane dake da alaƙa da gwamnatin Iran da suke bayyana kansu a matsayin farar hula ne a shafukan sada zumunta, suna yunƙurin ƙarfafa gwiwara masu zanga-zanga, har suna ba su kuɗaɗe.

Kakakin Fadar White House Karine Jean-Pierre ta ce 'yancin faɗin albarkacin baki na da muhimmanci ga dimokraɗiyyar Amurka, sai dai gwanati na da alhakin gargaɗin 'yan ƙasarta kan tasirin wasu daga ƙasashen waje.

"Amurkawa daga kowane ɓangare da suke aiki da zuciya ɗaya, suna ƙoƙarin bayyana ra'ayinsu na ƙashin kansu kan rikicin Gaza. Idan aka yi amfani da 'yancin bayyana ra'ayoyi mabambanta cikin lumana hakan abu ne mai muhimmanci ga dimokraɗiyyarmu," kamar yadda ta bayyana,

"A lokaci guda kuma, gwamnatin Amurka na da alhakin gargaɗin Amurkawa dangane da mummunan tasiri daga waje... Za mu ci gana da tona asirin duk wani yunƙuri na yi wa dimokradiyyarmu ƙafar ungulu kamar yadda muke yi a yau.

#