Sport
Dollar
39,1011
0.04 %Euro
44,4609
0.52 %Gram Gold
4.202,2600
1.92 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Ana zargin Kabila a DRC da aikata laifukan cin zarafin ɗan’adam, musamman goyon bayan tawaye a gabashin ƙasar, ciki har da rawar da ake zargin ya taka a kisan gilla na fararen hula da ma'aikata
Majalisar Dattawan Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ta kada kuri'a da rinjaye a daren Alhamis don cire rigar kariyar tsohon shugaban ƙasa Joseph Kabila, bisa zargin alaƙarsa da ƙungiyar 'yan tawaye ta M23.
Ana zargin Kabila a DRC da aikata laifukan cin zarafin ɗan’adam, musamman goyon bayan tawaye a gabashin ƙasar, ciki har da rawar da ake zargin ya taka a kisan gilla na fararen hula da ma'aikata. Gwamnati ta kuma ɗauki matakin dakatar da jam'iyyarsa ta siyasa tare da kwace kadarorin shugabanninta.
Kabila, wanda ya musanta duk wata alaƙa da ƙungiyar 'yan tawaye, ya sauka daga mulki bayan kusan shekaru 20 a kan karagar mulki a shekarar 2018, sakamakon zanga-zangar jama'a. Tun daga ƙarshen 2023, yana zaune a ƙasar Afirka ta Kudu.
Majalisar dattawan ta amince da cire rigar kariyar Kabila bayan an yi ƙuri’ar sirri inda mutum 88 suka amince da cire rigar kariyar sai kuma mutum biyar ba su amince ba.
Tawayen M23
Kabila ya nuna sha'awar dawowa Kongo don taimakawa wajen samo mafita ga rikicin da ke gabashin ƙasar, inda 'yan tawaye na M23 suka mamaye manyan yankuna.
Washington na matsa lamba don cim ma yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu kafin ƙarshen wannan bazara, tare da yarjejeniyoyin ma'adinai da ake sa ran za su kawo biliyoyin daloli na jarin kasashen Yamma zuwa yankin, in ji Massad Boulos, babban mai ba da shawara kan harkokin Afirka ga Shugaban Amurka Donald Trump, a wata hira da Reuters a farkon wannan watan.
Kabila ya hau mulki a shekarar 2001 bayan kisan mahaifinsa. Ya ƙi sauka daga mulki lokacin da wa'adinsa ya ƙare a hukumance a shekarar 2016, wanda ya jawo zanga-zangar da ta yi sanadiyar mutuwar mutane, kafin daga bisani ya amince ya bar ofis bayan zaɓen 2018.
Comments
No comments Yet
Comment