Dollar

39,0302

0.28 %

Euro

44,3529

0.69 %

Gram Gold

4.222,2900

2.4 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Kakakin kamfanin haƙar ma’adanan na Sibanye ya ce duka ma’aikatan suna cikin ƙoshin lafiya kuma mun san inda suke, sannan kamfnain yana ƙoƙarin tura musu da abinci.

Masu hakar ma’adanai kusan 300 sun makale a karkashin kasa a Afirka ta Kudu

Kamfanin haƙar ma’adanai na Sibanye Stillwater ya ca ana ƙoƙarin ceto mutane 289 da suka maƙale a wajen haƙar ma’adanan zinare na kamfanin da ke Kloof kusa da birnin Johnnesburg.

“Muna tabbatar da cewa an samu haɗari a Kloof 7, kuma mun duƙufa wajen ƙoƙarin samar musu da hanyar fitowa, inda daga nan kuma za mu fito da ma’aikatan,” kamar yadda kakakin kamfanin na Sibanye ya bayyana a ranar Juma’a.

Kakakin ya ce duka ma’aikatan suna cikin ƙoshin lafiya, kuma mun san inda suke, sannan kamfnain yana ƙoƙarin tura musu da abinci.

“Muna fatan cewa za a warware matsalar zuwa tsakiyar ranar yau,” a cewar kakakin.

Tun da farko, Ƙungiyar Masu Haƙar Ma’adanai ta ƙasar (NUM) ta ce ta samu rahotannin hatsarin, wanda ya faru da misalin ƙarfe goma na dare a ranar Alhamis.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#