Dollar

38,8828

0.03 %

Euro

44,0719

-0.03 %

Gram Gold

4.137,1600

-0.14 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

ECOWAS ta ce shirye-shiryen kafa “rundunar yaƙi da ta’addanci a yankin” da aka daɗe ana jira “sun kankama” yayin da Yammacin Afirka ke yaƙi da farfaɗowar hare-haren ‘yan ta’adda.

ECOWAS na duba yiwuwar kafa runduna yayin da hare-haren ‘yan bindiga ke kara yawaita

Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka ECOWAS ta faɗa a ranar Laraba cewa, shirin kafa rundunar yaƙi da ta'addanci da aka daɗe ana jira a yankin, ya kankama, a daidai lokacin da yankin ke fama da hare-haren 'yan ta’adda. 

Hare-hare a ƙasashen Benin da Najeriya a baya-bayan nan sun addabi yankin, inda masu tada kayar baya ke amfani da rashin jituwar da ke tsakanin mambobin ƙungiyar ECOWAS da Mali, Nijar da Burkina Faso, waɗanda suka fice daga ƙungiyar a farkon wannan shekara.

Yayin da ƙungiyoyin 'yan ta’adda a yankin Sahel da ke fafatawa a sassan iyakokin yankin mai girman gaske, janyewar ta haifar da koma-baya ga haɗin gwiwa tsakanin sojojin yankin.

Shugaban Hukumar ECOWAS Omar Alieu Touray ya bayyana a wata hira da kafar yaɗa labarai ta France 24 da aka buga a ranar Larabar da ta gabata cewa, "Ƙasashen sun nuna shirinsu na bayar da gudunmawar sojoji."

Tara kuɗi 

"Ana sa ran ministocinmu na harkokin kudi da tsaro za su gana kafin tsakiyar watan Yuni domin su tantance hanyoyin da za a samar da kudade ga rundunarmu ta yaki da ta'addanci a yankin."

Ministan tsaron Najeriya Mohammed Badaru ya faɗa a watan Maris cewa rundunar za ta tabbatar da tsaron yakin da kare jama’a. 

Sama da mutane 100 ne ‘yan ta’adda suka kashe a watan Afrilu kaɗ ai a arewa maso gabashin Najeriya, a hare-haren da aka kai kan al’ummomin yankin da sansanonin sojoji. Hare-haren da aka ci gaba da kai wa a wannan watan sun kara nuna girman matsalar.

Har ila yau, 'yan ta'adda masu alaka da Al-Qaeda sun zafafa kai hare-hare a kan da sojoji kasar Benin mai makwabtaka, inda suka kashe sojoji 54 a watan jiya.

Hadin gwiwar jihohin Sahel

Gwamnatin Benin dai ta dora alhakin kai hare-hare a yankunanta da tashe tashen hankula kan ‘yan ta’adda daga kasashen Nijar da Burkina Faso, wadanda suka dade suna fama da tashe tashen hankula.

Touray ya ce, rashin jituwar dangantaka tsakanin ECOWAS da gwamnatocin mulkin soja na Mali, da Nijar da Burkina Faso - wadanda suka kafa kungiyarsu mai suna Gamayyar Kasashen Sahel (AES) - na kawo cikas ga kokarin tsaron yankin.

A watan Maris ne Nijar ta fice daga rundunar hadin gwiwa da a kafa da hadin gwiwar Najeriya da Kamaru da kuma Chadi domin yaki da ‘yan ta’adda a kewayen tafkin Chadi – wanda ya kawo cikas ga sintiri a kan iyakokin kasar da musayar bayanan sirri.

Touray ya ce "Babban abin damuwa ne a gare mu, domin mun yi imanin rashin hadin kai zai sa mu sha wahala wajen hada kai don yaki da rashin tsaro, ciki har da ta'addanci."

Tsaron yanki

"Ko da (kasashen AES) sun yanke shawarar ficewa daga ECOWAS, ya kamata a samar da hanyar da za mu hada kai don tabbatar da tsaron yankin."

Bisa kididdigar da Cibiyar Lura da Ayyukan Ta'addanci ta duniya ta fitar, yankin Sahel shi ne cibiyar tashe-tashen hankula a duniya a shekarar 2024, inda a nan ne aka samu rabin mace-macen da ke da nasaba da tsattsauran ra'ayi.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#