Dollar

38,9253

0.13 %

Euro

44,0630

-0.08 %

Gram Gold

4.127,7500

-0.37 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

'Yan sandan sun ce "labarin ƙaryar", wanda tuni aka cire shi daga shafin nasu, wasu masu kutse ne suka wallafa shi tun farko.

An yi wa shafin rundunar 'yan sandan Tanzania kutse an sanar da mutuwar Shugabar Ƙasa Samia

Shafin X na 'yan sandan Tanzaniya ya fuskanci kutse inda aka wallafa wani labari na ƙarya kan mutuwar Shugabar Ƙasa Samia Suluhu Hassan.

‘Yan sanda sun bayyana cewa wannan “labari na karya da yaudara”, wanda aka cire daga baya, wasu masu kutse ne suka wallafa shi. Hukumar ba ta bayyana sunan waɗanda ake zargi ba.

Haka kuma, tashar YouTube ta Hukumar Haraji ta Tanzaniya ta fuskanci irin wannan hari, kamar yadda wasu kafafen labarai na Tanzaniya suka ruwaito, wanda ya haifar da fargabar cewa akwai haɗin gwiwar kai hare-haren na intanet kan hukumomin gwamnati.

Duk da haka, hukumomi sun tabbatar da cewa an shawo kan lamarin.

Wannan hari ya faru ne a daidai lokacin da ake fuskantar yanayi mai cike da rashin tabbas a siyasar ƙasar Gabashin Afirka, wadda za ta gudanar da zaɓuka daga baya a wannan shekara.

Shugaba Samia Suluhu Hassan ta hau mulki ne a shekarar 2021 bayan rasuwar wanda ya gabace ta, John Magafuli. Ita ce mataimakiyarsa kafin rasuwarsa.

Akwai raɗe-raɗin cewa za ta tsaya takara a zaɓen da ke tafe, amma ba ta bayyana niyyarta a hukumance ba tukuna.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#