Dollar

38,9222

0.13 %

Euro

44,0675

-0.07 %

Gram Gold

4.123,2100

-0.47 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Minsitan cikin gida na Libya ya ce an gano gawawwakin ne a wajen adana gawawwaki a wata mutuware a Asibitin Abu salim a birnin Tarabulus

An samu akalla gawawwaki 58 da ba a tantance su ba a wani asibiti a Libya

An gano aƙalla gawawwaki 58 da ba a san ko su wanene ba a ranar Litinin a wani asibiti da keTarabulus ko Tripoli wanda ke ƙarƙashin ikon wata ƙungiyar 'yan bindiga da aka kashe shugabanta a makon jiya, in ji ma'aikatar cikin gida.

An gano gawawwakin ne a cikin firij ɗin ajiyar gawa na Asibitin Abu Salim da ke unguwar Abu Salim mai cunkoson jama'a, bayan rahoton da aka samu daga asibitin, in ji ma'aikatar cikin gida a wata sanarwa.

Ma’aikatar ta wallafa hotunan gawawwakin da aka sanya lambobi aka kuma rufe fuskarsu, suna nuna gawawwaki a cikin yanayi daban-daban na ruɓewa a kan makarar ƙarfe da gadaje. Wasu daga cikin gawawwakin sun kone. Ana gudanar da bincike don gano ko su wanene waɗanda suka mutu.

“Ya zuwa yanzu, an binciki gawawwaki 23, kuma an ɗauki dukkan matakan doka da suka wajaba, ciki har da rubuta bayanai da tattara samfurori,” in ji ma'aikatar.

Ganowa ta biyu

A baya Abu Salim waje ne na wata ƙungiyar 'yan bindiga da aka sani da Stabilisation Support Apparatus (SSA), wadda aka kashe shugaban ta, Abdulghani Kikli, wanda aka fi sani da Ghaniwa, a cikin wani yanayi da ba tabbatar da shi ba a ranar 14 ga Mayu.

Kisan Kikli ya haifar da mummuna koma baya ga ƙungiyar SSA a karawar da su ke yi da ɓangarorin da ke goyon bayan Firayim Minista Abdulhamid al-Dbeibah na Gwamnatin Haɗin Kan Ƙasa (GNU) da aka amince da ita ta duniya.

A ranar Talata, Dbeibah ya ba da umarnin a rushe ƙungiyoyin 'yan bindiga, abin da ya haifar da faɗa mafi muni da Tripoli ta gani cikin shekaru tsakanin ƙungiyoyin 'yan bindiga biyu. Faɗan ya yi ajalin aƙalla fararen hula takwas, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya.

Gawawwakin da aka gano a ranar Litinin su ne na biyu da ba a san ko su wanene ba da aka gano a 'yan kwanakin da suka gabata. A ranar Asabar, jami'ai sun ce an gano gawawwaki tara a cikin firij ɗin ajiyar gawa na Asibitin Al-Khadra, wani asibiti da SSA ke iko da shi a unguwar Abu Salim.

Ƙungiyar 'yan bindigar ba ta bayar da rahoton gawawwakin ga hukumomin da suka dace ba, in ji ma'aikatar cikin gida.

A ranar Asabar Dbeibah ya ce kawar da ƙungiyoyin 'yan bindiga wani “aikin da ke ci gaba” ne, yayin da yarjejeniyar tsagaita wuta bayan faɗan makon da ya gabata ta ci gaba da aiki.

GNU ta wallafa wani bidiyo a ranar Litinin da ke nuna motocin rushe gini suna rushe sansanin da ake kira 77 camp, ɗaya daga cikin manyan wuraren da SSA ke iko da su. Za a mayar da sansanin ya zama filin shakatawa na ƙasa.

Tun bayan kifar da tsohon shugaban ƙasa Muammar Gaddafi a 2011 da goyon bayan NATO, Libya ba ta samu kwanciyar hankali ba. Ƙasar ta rabu a 2014 tsakanin ɓangarorin gabas da yamma, duk da cewa an daina gagarumin yaƙi sakamakon yarjejeniyar tsagaita wuta a 2020.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#