Dollar

38,9155

0.1 %

Euro

44,0559

-0.12 %

Gram Gold

4.120,8800

-0.53 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Kungiyar Masu Samar da Makamashi Mai Tsafta ta ce arzikin makamashin hasken rana da iska da Turkiyya ke da shi na iya kawo zuba jarin dala biliyan 80 tare da taimakawa wajen cike gibin makamashi a kasar.

Turkiyya na da manufar samar da GW 120 na makamashi mai tsafta nan da 2035

Turkiyya na da manufar kara yawan makamashinta mai tsafta zuwa megawatt 120,000 nan da 2035, in ji Yusuf Gunay, SHugaban Kungiyar Masu Samar da Makamashi Mai Tsafta a Turkiyya.

Da yake karin haske kan cigaban da aka samu a fannin makamashi, Gunay ya lura da cewa Turkiyya na da arzikin hasken rana da iska. “Dole ne a yi amfani da wannan arziki ta hanyar da ta dace,” in ji shi.

Wannan muhimmin cigaba ya faro ne tare da kafa Hukumar Kula da Kasuwancin Makamashi (EPDK), wadda ke karfafa gwiwar amfani da arzikin da ake da shi a cikin gida.

Karfin hasken rana da iska a Turkiyya

Gunay ya jaddada cewa makamashi mai tsafta na daya daga muhimman hanyoyin magance gibin makamashin da ake shigo da shi daga waje. Ya ce Turkiyya ce kasa ta 5 a Turai, ta 11 a duniya wajen samar da makamashi mai tsafta, musamman daga hasken rana da iska.

“Dole mu ci gaba da wannan aiki tare da kawata shi da makamashi mai sabuntuwa,” in ji shi.

Ya jaddada cewa karfin hasken rana da iska na Turkiyya ya fi na kasashen Turai da dama.

“A yanzu, kashi 40 na lantarki da muke samarwa na zuwa ne daga makamashi mai tsafta. Manufarmu ita ce nan da shekarar 2035 mu samar da megawatt 120,000.

“Wannan na bukatar zuba jarin dalar Amurka biliyan 80. A yayin da aka yi nasara kan wannan, zai bayar d agudunmowa babba ga tattalin arziki.”

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#