Sport
Dollar
38,9183
0.11 %Euro
44,0422
-0.13 %Gram Gold
4.120,4400
-0.54 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Kocin Manchester United, Ruben Amorim ya ce yana da imanin kan ƙarfinsa na kawo gyara a ƙungiyar, duk da cewa a shirye yake ya ajiye aiki bayan da suka gaza ɗaukar kofin Europa League.
Kocin Manchester United, Ruben Amorim, ya bayyana cewa idan Manchester United ba sa buƙatar ci gaba da aiki tare da shi, zai bar ƙungiyar "a washegari" wasan ƙarshe na gasar Europa, inda suka sha kaye a hannun Tottenham.
Amorim ya ce zai yi karɓi sallama ba tare da ya nemi diyya, wanda ke nuni da yadda ya amsa laifin gazawarsu ta ɗa ga kofin a wasan da aka yi a binin Bilbao na Sifaniya a daren Laraba, 21 ga Mayu 2025.
An doke Man United bayan da ɗan wasan Tottenham, Brennan Johnson ya zuraƙwallo guda ana dab da tafiya hutun rabin lokaci, wadda United ta gaza ramawa har aka tashi wasan.
Wannan rashin nasara ya ƙara dagula kakar wasar Man U, bayan da tarin matsaloli da suka haifar mata da gaza taka rawar gani a sauran gasannin.
United za ta ƙare kakar gasar Firimiya ta bana tana mataki mafi rauni, wanda rabonsu da yin ƙasa haka tun a shekarar 1974.
Sai dai duk da wannan ƙamfar tagomashi tun bayan da ya karɓi ragamar ƙungiyar daga hannun Erik ten Hag a Nuwamba, Amorim ya shaida wa manema labarai cewa zai ci gaba da tsayawa kan bakarsa na jagorantar ƙungiyar.
‘Za iya daidaita lamura’
Ruben Amorim, wanda tsohon kocin Sporting Lisbon ta Portugal ne, ya ce har yanzu yana da yaƙinin cewa zai iya daidaita abubuwa a Old Trafford, amma zai bar ƙungiyar idan ba a son ya tsaya.
"Idan shugabanni da masoya suna ganin ba ni ne mutumin da ya dace ba, zan tafi washegari nan, ba tare da wata magana kan diyya ba," in ji Amorim.
"Amma ba zan yi murabus ba. Ina da cikakken ƙwarin gwiwa a aikina. Kuma kamar yadda kuke gani, ba zan canja tsarin da nake gudanar da abubuwa ba."
Sai dai Amorim ya ƙi yin magana kan makomar ƙungiyar, yana mai cewa United na buƙatar "fuskantar rashin nasarar da kuma raɗaɗin kaye a wannan wasan."
Comments
No comments Yet
Comment